Dubun masu fasakwaurin mai ta cika
Wata kotu a Legas a ranar Talatar da ta gabata, ta yanke wasu direbobin jirgin ruwa, wadanda suka yi dakon mai na sata hukuncin biyan tarar miliyoyin Naira ko zama a gidan kaso na shekaru masu yawa. Direbobin jirgin ruwan su tara, wadanda ’yan yankin Asiya ne, ’yan kasar Philippines, 4 ’yan kasar Bangaladash 5; […]
Wata kotu a Legas a ranar Talatar da ta gabata, ta yanke wasu direbobin jirgin ruwa, wadanda suka yi dakon mai na sata hukuncin biyan tarar miliyoyin Naira ko zama a gidan kaso na shekaru masu yawa.
Direbobin jirgin ruwan su tara, wadanda ’yan yankin Asiya ne, ’yan kasar Philippines, 4 ’yan kasar Bangaladash 5; an kama su da laifin fasakwaurin mai na sata ne a watan Mayu a gabar tekun Legas, dauke da danyen mai da ya kai tan 3,423.
Kotun ta ba su zabin biyan tarar Naira miliyan 20 dukkaninsu ko zaman wakafi a gidan yari na kimanin shekara biyar.
Najeriya dai na tafka asarar biliyoyin Daloli a kowace shekara sakamakon mugunyar ayyukan masu fasakwaurin danyen mai.