Dubun matar da ake zargi da satar yara ta cika a Jihar Nasarawa
Matar da hada baki wasu wajen sace yaron mai shekara uku a duniya.
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta ce ta yi nasarar cafke wata mata da ake zargi da sace wani karamin yaro mai shekara uku a duniya.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Adesina Soyemi ne ya bayyana hakan yayin da aka gabatar da matar da wasu mutum 18 da ake zargi ga manema labarai, a Lafiya, babban birnin Jihar, ranar Laraba.
- Gwamnatin Kano ta rufe ofishin lauyan Shekarau
- Mutum na farko ya kamu da kwayar cutar Omicron a Saudiyya
Soyemi ya ce rundunar ’yan sandan ta yi nasarar cafke matar ne a unguwar Garaku da ke Karamar Hukumar Kokona a Jihar.
Ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya gano yadda matar ta hada baki da wasu yayin sace yaron da niyyar sayar da shi ga wani mutum a Jihar Enugu.
A cewarsa, an yi safarar yaron zuwa Jihar Enugu, amma ba su yi nasarar sayar da shi ba, wanda hakan ne ya sa suka dawo da shi Jihar Nasarawa.
“Wanda ake zargin sun tsere, amma an yi nasarar cafke wasu daga cikinsu, sai dai mutum daya ya tsere,” cewar Soyemi.
Ya ce rundunar na ci gaba da kokari don cafke mutum dayan da ya tsere.
Kazalika, Kwamishinan ’yan sandan ya ce ragowar mutum 18 da ake cafke a Jihar, ana zarginsu ne da aikata laifukan da suka shafi fyade da tsafi da safarar miyagun kwayoyi.
Ya ce dukkansu an mika su zuwa babban sashen bincike da ke hedkwatar rundunar ’yan sandan Jihar, don gudanar da bincike yadda ya kamata.