Dubun matasa ’yan kungiyar asiri ta cika a Kalaba
Akalla wasu matasa goma sha biyu ne rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ke garkame da su, sakamakon zarginsu da laifin hana birnin Kalaba sakat kuma ake kyautata zato ’yan kungiyar asiri ce kuma ana ci gaba da yi masu bincike, nan ba da jimawa ba za su gurfana gaban kuliya. Su dai wadannan matasa, an […]
Akalla wasu matasa goma sha biyu ne rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ke garkame da su, sakamakon zarginsu da laifin hana birnin Kalaba sakat kuma ake kyautata zato ’yan kungiyar asiri ce kuma ana ci gaba da yi masu bincike, nan ba da jimawa ba za su gurfana gaban kuliya.
Su dai wadannan matasa, an ce kodayaushe suna yawan fada tsakaninsu da sauran kungiyoyi da ba su ga maciji. Ba ta tsaya nan ba har fyade da aikata fashi da makami suna yi wa jama’a, lamarin da ya addabe su kafin dubun nasu ta cika. Binciken na ’yan sanda kamar yadda kakakinsu Hogan Bassey ya shaida wa Aminiya, akasarin matasan da aka kama sun fito ne daga kungiyoyin asiri daban-daban da suka hada da Black Ade da kungiyar KK da ta bikings.
Jami’in ’yan sandan ya bayar da sunayen matasan da ake zargi kamar haka Benedict Udoka, Paul Asukuo, Anthony Orim, Francis Omang, EtimNsa, Effiong Edet, Bassey Orok, Eyo Bassey, Eno Bassey, Umoh Ekpo, Emmanuel Daniel, Paulinus Edem da Christopher Undie .
A karin bayani, mutum biyu da aka kama, inji DSP Bassey, ya ce suna aiki ne da Ma’aikatar Kula Da Zirga-Zirgar Ababen Hawa, an kuma damke su a wata mashaya da aka same su suna holewarsu, suna cin naman kare a Kalaba.
Da suke yi wa Aminiya bayanin zargin da ake masu, Benedict Udoka da Effiong Edet sun ce: “Mun je mahadar ce muna cin abinci sai suka ga wata leda kusa da mu, koda muka duba sai muka ga cikinta akwai wata ’yar karamar bindiga. Muka ankarar da maigidan abincin, wanda daga bisani suka ce mana wani ne ya mance ta zai dawo amma tun da ga ’yan sanda can bari su kai masu. Daga nan sai musu ya kaure tsakaninmu, lamarin da ya jawo hankalin ’yan sanda suka zo har wurin suka tafi da mu.” Inji su.