Dubun wadansu ’yan fashi ya cika a Kurosriba
Rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ta gabatar wa manema labarai wasu kasurguman ’yan fashi da makami da kuma wasu matasa ’yan kungiyar asiri da suka addabi jihar suka, hana mata sakat.Daga cikin masu laifin da aka gabatar har ma da wasu maharba biyu da suka ce sun zo daga Kano yin harbin ungulu a dajin […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ta gabatar wa manema labarai wasu kasurguman ’yan fashi da makami da kuma wasu matasa ’yan kungiyar asiri da suka addabi jihar suka, hana mata sakat.
Daga cikin masu laifin da aka gabatar har ma da wasu maharba biyu da suka ce sun zo daga Kano yin harbin ungulu a dajin garin Ikom. Kodayake daya daga cikinsu ya ce shi mutumin garin Gaya ne na Jihar Kano, dayan kuma ya ce shi dan Jihar Jigawa ne daga garin Ringim.
Bayan da Kwamishinan ’yan sandan jihar ya gama yi wa ’yan jarida bayanin irin namijin kokarin da jami’ansa suka yi na cafke wadanda ake zargi, Aminiya ta gana da maharban biyu.
Farko, Musa dantanimu, wanda daga bisani ya ce sunansa Tanimu Yahaya Ringim ya ce, sunan kauyensu Zangon Kanya a Jihar Jigawa. “Ni baushe ne, ina yawon daji muka hadu da ’yan sanda, suka kama mu, ni da abokina. Babu wani laifi da aka same mu da shi, sai wannan farauta da muke yi kuma ba su gaya mana wani laifin da suke zarginmu da aikatawa ba. Mu dai maharba ne.” Inji shi.
Shi kuma Uzairu Abdu Gaya ya ce: “Ni harbin ungulu na zo yi, irin wadda ake amfani da sassan jikinta ana maganin shanyewar barin jiki. To, mun je wurin sarkin gargajiya muka ce masa mu mafarauta ne, ga abin da muka zo farauta. Ya ce to mu zagaya mu gani, idan akwai ko ma babu in mun dawo sai mu ba shi kudin da zai sha barasa. Muka ce mu ba mu da kudi, kafin mu dawo daga daji shi wannan sai ciwonsa na hawan jini ya tasar masa. Sai muka taho, mun zo zamu shiga gidansa da yake na bakin kogi, sai muka hadu da ’yan sanda, suka kama mu.”
Duk da sun fito daga Arewa ne, an tambaye su ko suna sane da halin tabarbarewar tsaro da kasar na take ciki, suka baro can suka zo Kurmi? A nan sai Abdu Gaya ya ce sun yi nadamar zuwa duk da ba su da labarin halin da ake ciki.
Ya zuwa rubuta wannan labara, an ingiza keyarsu zuwa garin Ikom domin ci gaba da yi masu bincike. Kwamishinan ’yan sandan Kurosriba, Henry Fadairo ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban na jihar kuma da zarar sun gama bincike, kotu za su tura su, domin fuskantar laifukansu.