Dubun wanda ake zargi da sace akuyar makwabcinsa ta cika
Da farko ya musanta, amma daga bisani aka ji kukanta a gidansa
Wani mutum mai suna Abdulfatai Olaganju mai shekaru 41 da ake zargi da satar akuyar makocinsa ya gurfana a wata kotun majistare da ke jihar Legas.
Dan Sanda mai gabatar da kara Insfekta M. Solomon ya ce mai akuyar, Murphy Chinedu ne ya kira ’yan sandan su binciko wanda ake zargin ya sace akuyar, bayan ya neme ta ya rasa.
- Hira da Yarinya Mai Baiwar Lissafi Da Ta Samu Tallafin Karatu Har Zuwa Jami’a
- An damke mutumin da ake zargi da yi wa marainiya mai shekara 7 fyade a Nasarawa
Ya ce yayin da suke bincike a gidan wanda ake zargin, da fari ya musanta, amma sai aka jiyo kukanta a gidan nasa daga bisani.
Lamarin dai ya faru ne a rukunin gidajen Kedeibu da ke unguwar Ijegun din jihar Legas, kuma dan sandan ya ce alamu na nuna wani abu ya ba akuyar da ya hana ta kuka lokacin da ya sace ta.
To sai dai wanda ake zargin ya ce akuyar da aka gani a gidan nasa ta shi ce ya siyo domin yin bikin Babbar Sallah ba ta makwabcin nasa ba.
Alkalin kotun Mai Shari’a O.I Williams ta ba da belin Abdulfatai kan Naira 100,000 da wanda zai tsaya masa da ya mallaki makamantansu, tare da dage karar zuwa ranar 24 ga watan Agustan 2022.