Dubun wani dan fashi da makami ta cika a Benin

kungiyar ’yan banga tare da hadin gwiwar Fulani makiyaya na yankin Ologbo sun samu nasarar kame wani gagararren dan fashi da ya addabi matafiya da masu dabbobi a yankin Kudu maso kudu. dan fashin da ake zargi, mai suna Buba Muhammadu, wanda aka fi sani da lakanin ‘Maisaje’ dan shekara 35, a bayaninsa ya ce […]

Dubun wani dan fashi da makami ta cika a Benin
Dubun wani dan fashi da makami ta cika a Benin

kungiyar ’yan banga tare da hadin gwiwar Fulani makiyaya na yankin Ologbo sun samu nasarar kame wani gagararren dan fashi da ya addabi matafiya da masu dabbobi a yankin Kudu maso kudu.

dan fashin da ake zargi, mai suna Buba Muhammadu, wanda aka fi sani da lakanin ‘Maisaje’ dan shekara 35, a bayaninsa ya ce shi mutumin Girei da ke Jihar Adamawa kuma dubunsa ta cika ne a lokacin da ya je dajin Ologbo tare da abokin ta’asarsa mai suna Iliya da dare, suka far wa garken shanu na wasu Fulani. Sun tasa shanun gaba za su kora su tafi kamar yadda aka ce suka saba.
Daga nan sai masu shanun suka kira shugaban ’yan banga, Alhaji Shu’aibu KT, suka nemi da ya kawo musu dauki, a inda suka fafata da wadannan mafasan. “Da muka kira ’yan bangan, muka labarta musu abin da muke ciki, a take suka kawo mana daukin gaugawa; suka ja daga da wadannan barayin sama da sa’a biyu cikin wannan dare, kafin suka samu nasarar cafke shi Maisaje. Shi kuwa Iliya da ya ga babu sarki sai Allah sai ya ranta a na kare kuma da yake a cikin duhun dare ne, ya samu ya tsere.” Inji Fulanin.
Kamar yadda Alhaji Shu’aibu ya tabbatar da kama dan fashin, ya ce: “Allah Ya taimaka mun kame shi babban mai suna Buba Maisaje, wanda a yanzu haka yana a hannu amma abokinsa Iliya ya arce kuma muna nemansa ido a rufe kuma duk inda ya kai ya boye, in sha Allahu sai mun kama shi. Don haka ina kira ga al’ummar wadannan yankuna da su ba mu hadin kai wajen zakulo inda ya buya da kuna fallasa duk irin wadannan miyagun, idan suka san mabuyarsu.”
Ya kara da cewa: “A yanzu haka idan mun kammala irin namu bincike a kan shi Maisaje, za mu mika shi ga hukumar ’yan sanda na hedikwatar jihar, domin gabatar da shi a gaban kotu.”
A ta bakin wanda ake zargi, Buba Maisaje yana mai cewa: “kaddara ce ta fada mani da tsautsayi, don haka ina rokonku da ku taimake ni wajen wadannan masu dabbobin su yafe mani, ba zan sake taba kayan wani ba da sunan sata ko fashi har abada”