Dubun wasu barayin shanu ta cika a Benin

Yan sanda na shiyyar Egba sun kame wasu matasa biyar da ake zargin barayin shanu ne a dajin cikin karamar Hukumar Uhonmwode da ke Jihar Edo.    Jami’in ’yan sanda, mai kula da shiyyar, Mista S. Obiuwebbi ya shaida wa Aminiya cewa wani mutum ne, wanda aka sakaya sunansa, ya labarta musu mabuyar barayin kuma suka […]

Dubun wasu barayin shanu ta cika a Benin

Wasu daga cikin shanun da aka sace aka kama barayinsuYan sanda na shiyyar Egba sun kame wasu matasa biyar da ake zargin barayin shanu ne a dajin cikin karamar Hukumar Uhonmwode da ke Jihar Edo.    
Jami’in ’yan sanda, mai kula da shiyyar, Mista S. Obiuwebbi ya shaida wa Aminiya cewa wani mutum ne, wanda aka sakaya sunansa, ya labarta musu mabuyar barayin kuma suka same su suna kokarin loda wasu shanu hudu (4) na wani dan kasuwa mai suna Alhaji Muhammadu. Yayin da ’yan sanda suka isa wurin, sai da suka yi artabu da barayin, inda suka samu nasarar cafke wasu daga cikinsu, sauran kuma suka arce cikin daji.
Daga cikin wadanda aka kama, inji jami’in, akwai Abdullahi da Muhammadu da dankwarai da Zakariya da Alaji da Maigaskiya, wadanda kuma bincike ya nuna su ne suka sace wasu shanu goma sha shida (16) na wani mai suna Alhaji Sharif Shuwa kimanin watanni biyu da suka wuce.
Jami’in ya bayyana cewa a halin da ake ciki suna tsare da wadanda aka kama din, “Har sai mun gama bincike a kansu, sauran kuma muna nemansu ruwa a jallo. Muna kira ga jama’ar wadannan kauyukan da su baiwa hukumar ’yan sanda hadin kai tare da fallasa miyagun a duk inda suka ji labarinsu”. Inji shi.