Dubun wasu ’yan ta’adda ta cika a Gombe
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta yi nasarar kama wasu matasa da ake zargin sun shahara wajen kashe-kashe inda a karshen makon shekaranjiya aka zarge su da kashe wani matashi mai sana’ar daukar hoto a garin Gombe mai suna Muhammad Bunu. Da yake nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta yi nasarar kama wasu matasa da ake zargin sun shahara wajen kashe-kashe inda a karshen makon shekaranjiya aka zarge su da kashe wani matashi mai sana’ar daukar hoto a garin Gombe mai suna Muhammad Bunu.
Da yake nuna wa manema labarai wadanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe Abdullahi Kudu Nma, ya ce a karshen makon shekaranjiya ne matasan su hudu suka kashe Muhammad Bunu, ba tare da ya yi musu komai ba.
Malam Kudu Abdullahi Nma, ya kara cewa jami’ansa sun yi nasarar cafke wadanda ake zargin ne a cikin mako biyu inda suka kama su da wasu matasa biyar da suka kware wajen yi wa mata kwacen jakakkunan hannu da wayoyin salula da gwala-gwalai.
daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Salisu Musa ya tabbatar wa wakilinmu cewa su ne suka kashe Muhammad Bunu mai daukar hoto a lokacin da fada ya shiga tsakaninsu da ’yan Unguwar Idi a yayin da suka kora wadancan din suna gudu, shi ma ganin haka ya fita da gudu sai suka dauka yana cikin wadanda suka kora da suka iske shi sai suka sassara shi.
Salisu Musa, ya ce ba su san cewa shi ba dan Kalare ba ne sai da suka sassare shi ya mutu a nan ne suka gane cewa mai daukar hoto ne baya cikin wadanda suka kora.
Ya ce da suka sassare shi ya mutu duk da cewa dai su ’yan Kalare ne amma ya ce a ransa bai ji dadin hakan ba, inda ya ce sun yi nadamar aikata wannan kisan da suka yi.
Har ila yau ’yan sandan sun sake kama wani babban dan Kalare mai suna Adamu Abubakar da ake wa lakabi da Baban Tudu, wanda ake zargi da yin kisan kai a bara kuma ya gudu har ‘yan sandan suka yi alkawarin tukuicin Naira dubu 250 ga duk wanda ya bada labarin da zai kai ga kama shi.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce suna cikin gudanar da ayyukansu ne kawai sai suka ci karo da Adamu Abubakar, suka kama shi domin tun a bara yaransa biyar da aka kama suna gidan yari.
Kwamishinan ’Yan sandan ya yi kira ga iyaye su rika tsawatar wa ’ya’yansu don gudun shiga kungiyoyin ’yan ta’adda musamman ma Kalare kuma ya ce ya yi alkawarin kawar da irin wadannan batagari a jihar baki daya.