Dubun wata mai safarar jarirai ta cika a Legas
Dubun wata mata ’yar kimanin shekaru 25 ya cika a lokacin da ta yi safarar jariri dan mako guda da haihuwa daga garin Onitsha a Jihar Anambra zuwa Jihar Legas domin sayar da shi.Matar mai suna Nkechi Obi, asirinta ya tonu ne a sa’ilin da direban motar da ta dauka haya daga garin Asaba a […]
Dubun wata mata ’yar kimanin shekaru 25 ya cika a lokacin da ta yi safarar jariri dan mako guda da haihuwa daga garin Onitsha a Jihar Anambra zuwa Jihar Legas domin sayar da shi.
Matar mai suna Nkechi Obi, asirinta ya tonu ne a sa’ilin da direban motar da ta dauka haya daga garin Asaba a Jihar Delta ya lura da ba ta iya shayar da jaririn ba a tsawon tafiyar da suka yi ta fiye da awanni 6; duk da kuwa kukan da yaron yake ta tsalawa. Hakan ne ya sa ya gano cewa ba danta ba ne, inda ya ankarar da jami’an ’yan sanda a daidai lokacin da ya shiga unguwar Oshodi a Jihar Legas; wadanda nan take suka kame ta.
A cewar Nkechi Obi, wata maigidanta ce mai suna Ngozi ta ba ta jinjirin domin sayar wa wata mata mai bukatar da namiji a Legas.
A yanzu dai matar da ta yi niyyar sayen yaron ta shiga komar ’yan sanda, wacce ta shaida cewa tana da ’ya’ya biyu mata kuma mijinta ne ya uzura mata, yana yi mata barazanar kara yin aure matukar ba ta haifi da namiji ba, wanda hakan ne ya sa ta yanke shawarar sayen jinjirin, domin ta maida shi danta.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Fatai Owoseni ya tabbatar da kame matan biyu da ake zargi da kulla haramtaccen cinikin sayar da jinjirin kuma ya ce rundunar tasu za ta fadada bincikenta a kan lamarin, duk da dai Ngozi ta arce bayan da ta sami labarin kame Nkechi Obi da rundunar ’yan sandan ta yi. Ya kuma sha alwashin hukunta duk wani mai hannu a lamarin, kana ya kara da cewa rundunar tare da hadin gwiwar hukumar tallafa wa iyalai na ba jinjirin kulawa ta musamman.