Dubun ’yan fashi da suka addabi Zuru ta cika
’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani da ake zargin gawurtaccen dan fashi ne mai suna Bitrus danbaba Danko da abokansa biyu da suka addabi jama’ar Zuru wajen tare hanyoyin Zuru zuwa Riba da Wasagu zuwa Dadinkowa Unashi da Riba zuwa Maga da Danko. A lokacin da Kakakin ’yan sandar jihar ASP Mohammed Mainagge […]
’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wani da ake zargin gawurtaccen dan fashi ne mai suna Bitrus danbaba Danko da abokansa biyu da suka addabi jama’ar Zuru wajen tare hanyoyin Zuru zuwa Riba da Wasagu zuwa Dadinkowa Unashi da Riba zuwa Maga da Danko. A lokacin da Kakakin ’yan sandar jihar ASP Mohammed Mainagge yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai da abokan fashinsa Mohammed Farida Dadinkowa da Abubakar Sadiku dan dan Sarkin Fulani Mammaga, ya ce an kama wadanda ake zargin suna fashin ne da kananan bindigogi kirar fistol biyu da adda daya. Sai kuma ya gabatar da wasu mutum biyu masu suna Obinna da Aliyu Kalgo da ake zargi da kwace wa bawan Allah Naira dubu 250, bayan ya karbo su daga banki. Ya ce mutumin ya ajiye motarsa ya shiga cikin bankin, sai suka samu wani tsohon takalmi suka soka masa kusa suka sanya a jikin tayar motarsa. Bayan ya wuce sai suka bi shi a baya suka ce masa tayarka ta yi faci sai ya tsaya, sai suka tsaya kusa da kofar motar sai daga guda ya je yana taya shi duba tayar shi kuma dayan sai ya sa hannu ya dauke kudin ya buga babur ya ce Alhaji sai an jima amma ga mai faci can. Ya ce bayan sun wuce ne sai wani mutum da ke kusa da wurin ya ce wa mai kudin masu babur din can sun dauki wani abu a cikin motarsa ko tare suke? Yana dubawa sai ya ga babu kudi, sai aka bi su aka kama su a wani gari mai suna Kola kimanin kilomita 10 daga Birnin Kebbi.