Dubun ’yan kungiyar asiri ta cika a Jihar Ogun
Rundunar ’yan sanda ta musamman mai yaki da ’yan fashi da makami Jihar Ogun ta yi nasarar kame wasu matasa ’yan kungiyar asiri ta Eiye a unguwannin Papa Landowners da Ewekoro, wadanda suka dade suna addabar al’ummar yankin da wasu sassa na jihar.Matasan ’yan kungiyar asiri su goma, wadanda suka hada da Opadola Olatunde, Sanni […]
Rundunar ’yan sanda ta musamman mai yaki da ’yan fashi da makami Jihar Ogun ta yi nasarar kame wasu matasa ’yan kungiyar asiri ta Eiye a unguwannin Papa Landowners da Ewekoro, wadanda suka dade suna addabar al’ummar yankin da wasu sassa na jihar.
Matasan ’yan kungiyar asiri su goma, wadanda suka hada da Opadola Olatunde, Sanni Afeez da sauran wasu guda takwas, sun shiga komar jami’an ’yan sanda ne a lokutan bukukuwan Kirismeti tat a gabata. Jami’an ’yan sandan sun gano muggan makamai a tare da ’yan kungiyar asirin, wadanda suka hada da bindigogi 2 kirar gida da wukake da adduna da kayayyakin tsafe-tsafe. Sun kuma amsa laifukansu, kamar kuma yadda jami’an tsaron suka ce suna ci gaba da tatsar bayanai daga wajensu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abdulmajeed Ali ya shaida wa Aminiya cewa tuni ya ba zaratan jami’an ’yan sandar jihar umarnin kame duk wani dan kungiyar asiri da sauran bata gari, don ganin an kawo karshen barazanar zaman lafiyar da suke yi wa ilahirin jihar. Ya kuma kara da cewa rundunar za ta kara fadada ayyukanta, a kokarinta na kare dukiya da rayukan al’umar jihar.