Dubun ’yan sanda ta cika kan sace N43m a hannun direba
Dubun wasu ’yan sanda huɗu ta cika kan sace Naira miliyan 43 da suka ƙwace a hannun wani direban kamfanin dakon kaya a Abuja
An dakatar da wasu ’yan sanda huɗu daga aiki kan zargin sace Naira miliyan 43 a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ana zargin ’yan sandan sun ƙwace kuɗin ne a lokacin da suka tsare direban ba bisa ka’ida ba.
’Yan sandan su huɗu sun haɗa da DSP Peter Ejike da Insfekta Ekende Edwin da Insfekta Esther Okafor da kuma Sakan Talabi Kayode, sun haɗa baki ne tare da ɓoye hujjojin da kuma wasu laifuka.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Ƙasa, ACP Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin, sun tsare direban kudin ba bisa ka’ida ba ne a lokacin da yake jigilar kuɗin a madadin waɗanda suka ba kamfanin dakon kaya da yake aiki (FATFAD Cargo), aikin a watan Agustan 2023.
Adejobi ya ce ’yan sandan sun ƙi bayyana Naira Naira miliyan 43.16 daga cikin kuɗin, inda suka bayar da rahoton miliyan 31.79 kaɗai.
Bayan masu kuɗin sun rubuta takardat ƙorafi ofishin shugaban ’yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike inda aka gano yadda suka karkatar da kuɗin inda suka yi ƙaryar cewa matsalar na’ura a yunƙurins na ɓoye abin da suka yi da kuma bayar da bayanan ƙarya.
Bayan sun ƙwace kuɗin ne suka kira kamfanin da cewa sun ƙwace Naira miliyan 31.79 a wurin direban, sannan suka nemi a ba su wani kaso daga cikin kuɗin domin su kashe maganar.
Hakan ne ya fusata kamfanin ya kai ƙara inda bayan bincike aka gano yadda suka karkatar da kuɗaɗen da kuma yadda suka yi ta yada labaran karya a intanet domin juya maganar.
Adejobi ya ce binciken ya gano cewa sun ɗauki hoton kuɗaɗen a lokacin da suka tsare direban, amma suka yi ƙaryar cewa wayar ta lalace, kuma daga baya ta ɓace, a ƙoƙarinsu na ɓoye hujjojin.