Duk abin da Ukraine ke ji da shi ta fuskar makamai ta tara ta samu — Rasha
Rasha tana da isassun tarin alburusai iri-iri.
Shugaba Vladimir Putin ya ce Rasha na da isassun harsasai da za ta iya tunkarar Ukraine har idan za ta yi amfani da makamai.
Putin ya yi wannan kashedi ne a wata hira da gidan talabijin na gwamnatin Rasha a yau Lahadi.
- Messi ya kulla yarjejeniyar shekara 2 da Inter Miami
- Kofin Duniya 2026: Yadda kasashen Afirka za su fafata wajen neman tikiti
Bayanai na cewa Ukraine ta fara samun tarin makamai daga Amurka, matakin da ya haifar da damuwa.
“Rasha tana da isassun tarin alburusai iri-iri,” in ji Putin a lokacin da yake magana da gidan talabijin na gwamnati.
Ukraine ta mallaki wasu makamai daga kasashen ketare,“Idan aka yi amfani da su a kanmu, za mu mayar da martani nan take inji shugaban Rasha.
Ya kara da cewa har yanzu Rasha ba ta yi amfani da makaman ba duk da cewa akwai karancin albarusai a wani lokaci.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch da dakarun Ukraine sun zargi Rasha da yin amfani da harsasai masu tarwatsewa a fagen daga.
Kasashe da dama ne suka haramta su musamman a Turai.