Duk abin da ya samu Buhari PDP za mu rike – APC

Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da wata talla da Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya dauki nauyin bugawa a wasu jaridun kasar nan da suka fito a ranar Litinin da ta gabata, inda ya nuna yiwuwar mutuwar Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar. Jam’iyyar ta bayyana tallar da cewa tana yi […]

Duk abin da ya samu Buhari PDP za mu rike – APC

Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da wata talla da Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya dauki nauyin bugawa a wasu jaridun kasar nan da suka fito a ranar Litinin da ta gabata, inda ya nuna yiwuwar mutuwar Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana tallar da cewa tana yi wa dan takararsu “fatan mutuwa” ne. Haka kuma ta zargi jam’iyyar PDP da cewa tana yi wa rayuwar Janar Buhari barazana, sannan kuma ta yi kunnen uwar shegu da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ’yan takara da ke cewa a yi yakin neman zabe cikin lumana ba tare da tashin hankali ko cin mutunci ba.
Daraktan Watsa Labarai Na Kwamitin Yakin Neman Zaben Janar Buhari, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce: “Duk abin da ya samu Janar Buhari, kafin ko lokacin ko bayan zabubbuka, to PDP za mu rike.”
Kwamitin yakin neman zaben na APC ya kuma shawarci Shugaba Jonathan da ya kula da al’amuran yakin neman zabensa kafin mabiyansa su jefa Najeriya cikin rikici.
Kuma roki dukkan magoya bayan Janar Buhari da ke fadin kasar nan da kada su kula abin da PDP ke cewa da nufin tunzura su, domin kuwa suna yin haka ne da nufin samun kafar da za ta sanya su yi wa dimokuradiyyar kasar nan kafar ungulu kafin ko kuma bayan zabubbukan da ke tafe.
Shehu ya ce, “Wannan ba karamin makirci ba ne da PDP ke shiryawa, wanda zai iya haddasa zubar da jinin al’umma ba dalili, sannan kuma ya haddasa asarar dukiya. Suna fatan mutuwa a kanmu, wannan ba siyasa ba ce. Don haka muna gaya wa magoya bayanmu da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka.
“Duk da cewa shi ma dan takara ne, hakkin Dokta Goodluck Jonathan ne har zuwa 29 ga Mayun bana, lokacin da za a rantsar da sabon Shugaban kasa, ya kikaye dukiya da rayukan al’ummar kasar nan.”
ACF ta yi Allah-wadai da batun
Ita ma kungiyar kare muradun Arewa ta bakin shugabanta Alhaji Ibrahim Commasie, ta bayyana cewa aniyar Gwamna Fayose za ta bi shi, domin shi ba Allah ba ne, kuma Allah ne kadai ya san wanda zai riga wani mutuwa.
Alhaji Commasie wanda tsohon dan Shugaban ‘yan Sanda ne na kasa, ya ce babu tunani a cikin kalaman na Fayose.
Ya kuma bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya ta waya a Kaduna. Ya ce,”Shi Allah ne, ko kuwa siyasa ce tasa shi yake irin wannan kalaman da babu tunani a ciki? To, aniyarsa za ta bi shi. Wannan ai surutun banza yake yi. Bai kamata ya rika irin wannan magana ba. Duk wani dan adam ai mutuwa ba a hannunsa take ba. Saboda haka idan burinsa shi ne ‘yan arewa su rika mutuwa a mulki sai dai shi ya mutu. Kuma ai mutuwa da rayuwa ta Allah ce, saboda haka babu wanda ya isa ya kashe wani idan ba kwanansa sun kare ba,” inji shi.
Game da ko akwai mataki da za su dauka a kungiyance, sai ya ce, ‘’al duk mai hankali dole ya dauki matakin yin Allah wadai da wannan magana ta gwamnar Ekiti, ba kawai sai ACF ba.’’