Duk da kukan talauci talakawan Najeriya na kara kiran waya
Kamfanin MTNA ya samu kudaden shiga a dalilin kiran waya da suka kai Naira biliyan 258.
A makon jiya ne, Shugaban Kamfanin Sadarwa na MTN, babban kamfanin sadarwa a Najeriya, ya shaida wa masu zuba jari cewa zuwa ranar 25 ga Afrilun bana, “Kimanin masu amfani da layukansu miliyan 60 ne suka gabatar da lambar katin dan kasa (NIN) ga kamfanin, wanda hakan na wakiltar kusan kashi 85 na masu amfani da layukan da aka ba su damar yin waya.
Kamfanin ya samu kudaden shiga a dalilin kiran waya da suka kai Naira biliyan 258 daga Naira biliyan 244.6 adadin da ya haura abin da suka samu a daidai wannan lokaci a bara.
- Har yanzu dana yana hannun ’yan bindiga – Farfesa Ango Abdullahi
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 57 a Bangladesh da Indiya
Kamfanin Airtel, an ruwaito yana da masu hulda da shi mutum miliyan 35.9 sannan kudin shigarsu a bangaren yin kira a waya ya karu idan an kwatanta da bara, inda a bana suka samu Naira biliyan 112.5 a tsakanin watan Janairu zuwa Maris, inda a bara suka samu Naira biliyan 103.3 a cikin watan uku na karshen shekara da ta gabata wato daga Oktoba zuwa Disamba.
Wannan adadi ya nuna cewa al’ummar kasar nan suna kara yawan kiran waya duk da kukan talaucin da suke yi.
A cewar Kamfanin MTN, karuwar kudin kiran wayar “ya habaka ne ta hanyar fadada hanyoyin samun abokan ciniki da kuma shirye-shiryen wayar tarho na karkara da kuma ingantaccen kayan aikinmu na daraja abokan huldarsu.”