Duk da man Dangote, wahalar fetur ta dawo a Abuja

Walahar man fetur ta dawo a Abuja duk da cewa manyan dullalansa sun fara sayen man Matatar Ɗangote, wanda ake sa ran zai magance matsalar.

Duk da man Dangote, wahalar fetur ta dawo a Abuja

Walahar man fetur ta dawo a Abuja duk da cewa manyan dillalansa sun fara sayowa daga Matatar Ɗangote, wanda ake sa ran zai magance matsalar.

An samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a ranar Talata da safiyar Laraba a Abuja, a yayin da wasu gidajen man ’yan kasuwa suka kasance a rufe.

Hakan na zuwa ne bayan a ranar Talata kakakin Ƙungiyar Manyan Dillalan Mai na Kasar (MEMAN), Huub Stokman, ya sanar cewa sun fara ɗaukar man Matatar Ɗangote.

Sai dai bai bayyana ko kai-tsaye daga Matatar Ɗangote suke saya ba, ko kuma wanda Kamfanin Mai na Ƙasa (NNNPC) ya saya daga matatar suke sayowa.

Amma rahotanni sun nuna cewa a cikin mako guda da ya gabata adadin man Matatar Ɗangote da dillalan suka ɗauka ya kai lita miliyan 50.

Amma daga ranar Talata zuwa safiyar Laraba an samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a Abuja a sakamakon karancin man.

Akasarin gidajen mai masu zaman kansu ba su buɗe ba, ’yan ƙalilan da suka buɗe, da na NNPC kuma na fama da cincirindon ababen hawa.

An samu dogayen layukan ababen hawa a babban gidajen man NNPC da NIPCO da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Zuba.

Hakazalika a gidan man AP da ke titin Aguiyi Ironsi a ƙwaryar birnin Abuja da kuma na AA Rano da ke unguwar Utako.

Wannan yanayin ya haifar damuwa ga masu hawa motocin haya a sassan Abuja, a yayin da masu sayar da man ta bayan fage suka wasa wuƙarsu, suka tsawwala farashi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7