Duk da rinjayen Erdogan akwai yiwuwar zuwa zagaye na biyu na zaben Turkiyya 

Da alama zaben shugaban kasar Turkiyya zai kai ga zagaye na biyu, duk da cewa shugaba Recep Tayyip Erdogan ke kan gaba da 4% a zagayen farko.

Duk da rinjayen Erdogan akwai yiwuwar zuwa zagaye na biyu na zaben Turkiyya 

Shugaban Turkiyya, Recep Erdogan

Da alama zaben shugaban kasar Turkiyya zai kai ga zagaye na biyu, duk da cewa shugaba Recep Tayyip Erdogan ke kan gaba da 4% a zagayen farko.

Bayan shafe shekaru 20 yana mulki, Erdogan da jam’iyyarsa na da kwarin gwiwar zai yi nasarar zuwa wa’adi na biyar.

Shi ma babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu ya yi ikirarin samun nasara  zagaye na farko.

Amma sakamakon zaben da bai kammala ba ya ba shi kusan kashi 45%, yayin da Mista Erdogan ya samu fiye da kashi 49% na kuri’un da aka kada.

‘Yan takara na bukatar fiye da kashi 50% domin samun nasara a zagayen farko.

Mista Erdogan na da karin karfin gwiwa, a yayin da yake neman tsawaita wa’adin shugabancinsa.

Ita ma jam’iyyarsa ta samu rinjaye a majalisar, kamar yadda alkaluman farko da kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayar.

Tsawon watanni dai jam’iyyun adawar kasar Turkiya sun yi hadaka domin ganin an kawo karshen shugaban Erdogan, wanda juyin mulkin da aka yi masa a 2016 bai yi nasara ba.

Kasashen Yammacin duniya suna sanya ido sosai kan zaben, domin Mista Kilicdaroglu ya yi alkawarin farfado da dimokuradiyyar Turkiyya da kuma alaka da kawayenta na NATO.

A daya hannun kuma, gwamnatin shugaba Erdogan mai tushe ta kishin Islama ta zargi kasashen yammacin duniya da yunkurin kifar da shi.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro