Duk da sukar takarar Musulmai 2, an ga malaman coci a wurin kaddamar da Mataimakin Tinubu

A baya dai sun ce za su kauracewa bikin

Duk da sukar takarar Musulmai 2, an ga malaman coci a wurin kaddamar da Mataimakin Tinubu

Tinubu lokacin da yake kaddamar da Kashim Shettima

Mutane sun cika da mamaki bayan sun ga fuskokin malaman coci, ciki har da masu matsayin Bishop-Bishop a wajen kaddamar da Sanata Kashim Shettima a matsayin Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu.

Taron dai ya gudana ne ranar Alhamis a dandalin Shehu Musa ’Yar’aduwa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Tun da farko dai, kafafen yada labarai sun cika da labaran suka iri-iri daga kungiyoyin mabiya addinin Kirista daban-daban da ke sukar lamirin APC kan tsayar da Musulmai biyu a takarar.

Kungiyoyin dai sun yi ta kiran shugabanninsu da su kauracewa wajen kaddamar da mataimakin dan takarar don nuna bacin ransu a kai.

Ko a ’yan makonnin da suka gabata, sai da mai magana da yawun shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), Fasto Adebayo Oladeji ya yi Allah-wadai da matakin na APC.

A wani labarin kuma, Babban Sakataren CAN na kasa, Rabaran Joseph Bade Daramola, ya bayyana zabin Shettima a matsayin ayyana yaki da Kiristocin Najeriya.