Duk da tsadar rayuwa an sami ƙaruwar masu zagayen Maulidi a Gombe

Duk da matsin tattalin arziki, an samu karin yawan makarantu da dalibai da suka halarci zagayen na bana.

Duk da tsadar rayuwa an sami ƙaruwar masu zagayen Maulidi a Gombe

Shugaban Makarantun Islamiyya na Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Nuhu, ya bayyana cewa kunci da tsadar rayuwa ba su hana dalibai  fitowa zagayen Maulidi ba.

Ya ce duk da matsin tattalin arziki, an samu karin yawan makarantu da dalibai da suka halarci zagayen na bana.

A cewarsa, adadinsu ya kai 167,302, banda waɗanda ba sa ƙarƙashin wata makaranta.

Alhaji Muhammad Nuhu ya ƙara da cewa a kowace shekara ana samun cigaba, musamman wajen gyara tare da tsabtace shirin.

A shekarun baya, ana samun matasa masu tayar da zaune tsaye suna fakewa da masu maulidi, amma bayan hada kai da jami’an tsaro da ’yan banga, an samu sauƙin matsalar a shekaru biyu da suka gabata.

A cewarsa, sun dauki jami’an tsaro na sirri sama da 50, tare da haɗin guiwar ’yan banga, jami’an tsaro, ’yan agaji, da kuma kwamitin tsaro na masu shirya zagayen, wanda hakan ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da tsaron mahalarta.

Har ila yau, ya bayyana cewa ko ’yan kasuwa masu sayar da kaya sun tabbatar da cewa a bana an sayi ɗinkunan anko da yawa.

Wannan ya nuna cewa tsadar rayuwa ba ta shafi fitowar al’umma a wannan zagaye na Maulidi ba.

Alhaji Muhammad Nuhu ya gode wa malaman makarantun Islamiyya da ɗalibansu bisa haɗin kai da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kawar da bata-gari da ke jawo wa masu zagayen Maulidi zagi da cin mutunci.

Wakilinmu ya kai ziyara kasuwar Gombe, inda ya tattauna da wasu ’yan kasuwa game da cinikin kayan Maulidi.

Wasu daga cikinsu sun tabbatar da cewa an sayi anko da yawa, yayin da masu ƙananan kaya suka ce su ma sun samu ciniki sosai, musamman ga waɗanda suka makara wajen samun ɗinkunan yadi, don haka sun sayi ƙananan kaya maimakon ɗinkunan.

NAFDAC ta gano wani jabun maganin malaria da ke yawo a Najeriya

Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane

An daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

An bai wa tsofaffin ’yan bindiga 6 shaidar tuba a Yobe