Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra’ila ta kashe Falasdinawa 8

An yi kisan ne duk da yarjejeniya tsagaita wuta da Hamas

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra’ila ta kashe Falasdinawa 8

Isra’ila ta kashe Falasdinawa kimanin 3,000 a luguden wutan da take yi a Zirin Gaza (Hoto: Zain Jaafar / AFP)

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa takwas, ciki har da wani ƙaramin yaro a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da ta cim ma tsakaninta da ƙungiyar Hamas.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ce ta tabbatar da hakan ranar Lahadi, inda ta ce ya zuwa yanzu, yawan mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaɓar ya tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 239.

Sojojin na Isra’ila dai sun harbe mutum biyar a birnin Jenin da yammacin Asabar, sannan da safiyar Lahadi kuma suka sake kashe wasu mutum uku.

Ma’aikatar ta kuma ce sojojin sun kuma hallaka wasu mutum shida a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na wafa ga rawaito cewa sojojin sun yi wa garin ƙawanya ta wurare daban-daban, inda suka riƙa harba bindigogi sannan suka mamaye asibitocin gwamnati da ofishin ƙungiyar Red Crescent.

Sai dai Kakakin sojojin Isra’ila ya ce suna nan suna nazari a kan rahotannin.

An kai harin ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana huɗu da aka cim ma tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza, inda aka kashe sama da Falasdinawa 15, ciki har da kananan yara sama da 6,000.

Ita ma Isra’ilq ta ce an kashe mata sama da mutum 1,200 a wani harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sannan aka kama Yahudawa kimanin 240.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja