Duk dan majalisar da ya ki yin aiki Za mu dawo da su – Gambo Bababa
Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma Shugaban kungiyar masu Magananin Gargajiya a Bauchi ta Kudu, Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana cewa aikin dan majalisar dokoki tun daga jiha zuwa sanatoci shi ne yin doka da sanya ido ga bangaren zartarwa. Ya ce amma […]
Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma Shugaban kungiyar masu Magananin Gargajiya a Bauchi ta Kudu, Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana cewa aikin dan majalisar dokoki tun daga jiha zuwa sanatoci shi ne yin doka da sanya ido ga bangaren zartarwa.
Ya ce amma duk da haka ya kamata su rika kyautata wa mutanen mazabarsu daga lokaci zuwa lokaci domin kowa ya san cewa akwai makudan kudi da ake ba su duk bayan wata uku. “Amma yanzu mun zuba musu ido zuwa nan da shekara ta 2016 watakila a samu sauyi mai amfani,” inji Gambo.
Gambo Bababa ya ce talauci ya yi tsamari a Jihar Bauchi saboda haka yana kira ga ’yan Majalisar Dokoki ta kasa da sanatoci da Gwamnan Jihar Barista Mohammad Abubakar su fahimci cewa sama da kashi 85 cikin 100 na magidanta a jihar ba sa iya cin abinci sau uku a rana. “Sakamakon yadda talauci ya addabi mutanen birni da karkara.Duk shugaban da yake son zaman lafiya da kwanciyar hankali ya zamo wajibi ya rika kyautata wa mata da matasa domin amfanin mulkin dimokuradiyya ke nan,” inji shi.
Gambo Bababa ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce duk shugaban da ya kuntata wa al’umma shi ma Allah Ya kuntata masa don haka ya kamata shugabanni su ji tsoron Allah su rika taimaka wa talakawansu da hanyar da za su ciyar da iyalansu.
Daga bisani ya bukaci Gwamna Mohammed Abubakar da ya yi wa Allah ya nada kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi da sauran masu tallafa wa Gwamna.