Duk inda kudadenmu suke a kwato su, `yan kasa a kara hakuri
A ranar Litinin din makon da ya gabata 18-01-15, aka ji Ministan Yada labaran kasar nan Alhaji Lai Mohammed, a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja babban birnin tarayya, ya fada wa duniya cewa, tsakanin shekarun 2006 zuwa 2013, wasu kusoshin kasar nan da suka samu kansu cikin rike amanar dukiyar kasar […]
A ranar Litinin din makon da ya gabata 18-01-15, aka ji Ministan Yada labaran kasar nan Alhaji Lai Mohammed, a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja babban birnin tarayya, ya fada wa duniya cewa, tsakanin shekarun 2006 zuwa 2013, wasu kusoshin kasar nan da suka samu kansu cikin rike amanar dukiyar kasar nan su 55, sun sace Naira tiriliyan 1.3, a cikin wa`adin shekaru bakwai rak. Wa`adin da ya kunshi kusan karshen zango na biyu na shugabancin Cif Olusegun Obasonjo da na shekaru uku na marigayi shugaban kasa Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa da na tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan.
Alhaji Lai ya bayyana filla-filla rukunnan mutane 55, da suka wawure wadancan makudan kudi, da yawan kudin da kowane rukuni ya sace, tsofaffin gwamnonin jihohi 15, sun wawure Naira biliyan 146.84, yayin da tsofaffin Ministoci hudu, da ake zarginsu da wawushe Naira biliyan7, sai wasu tsofaffin ma`aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi su 12, da Ministan ya ce sun sace Naira biliyan 14. Wani rukunin mutane da Ministan yada labaran ya bayyana su ne, tsofaffin ma`aikatan Bankunan kasuwanci, da ya ce wasu 8,ana zarginsu da yin fincen kudin masu ajiya har Naira biliyan 524, ya yin da rukunin mutane na karshe da suka yi wa kudaden kasar nan wawurar da ba ita ba ce ba, su ne wasu 11, da suka fito daga rukunnan `yan kasuwa, su kuma ya ce sun sace Naira biliyan 653.
Bisa ga kiyasin kashe kudade na Hukumar bayar da lamuni ta duniya, wato IMF, in ji Ministan, wadannan kudi sun isa a gina titi mai tsawon kilomita 635.18km, ko a gina maka-makan asibitocin zamani 36, daya a kowace jiha, ko manyan makarantu 183, ko ilimantar da yara 3,974, tun daga ilimin Firamare har ya zuwa na gaba da Sakandare, ko da kuwa za a kashe wa kowannensu Naira miliyan 25.2. Wadancan makudan kudi in ji Ministan za su isa a gina gidaje masu dakuna bi-biyu har dubu 20 da 062, a kasar nan.
Wannan bayani na irin yadda wasu da suke jin sun isa bisa amanar da suka rike, suka kuma rinka watanda da dukiyar al`ummar kasar nan, yana nunawa mai karatu cewa, ba yau aka fara yin cin kaca ba da dukiyar al`ummar kasar nan, musamman idan ka bi sawun irin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatoci irin na Janar Murtala/Obasonjo (wadda ita ta fara wannan yakin) da ta Janar Muhammadu Buhari da ta Janar Sani Abacha da ta farar hula ta Cif Olusegun Obasonjo, (Obasojon da ya kafa Hukumar yaki da ta`annati da kudaden jama`a ta EFCC da Kotun da`ar ma`aikata ta CCBC) da wannan sabon yakin da gwamnatin farar hula ta shugaba Buhari ta dukufa akai tun ma kafin bayyanar watanda da Dala biliyan biyu ($2.1) na kudin sawo makamai da a ke zargin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki ya yi. Wannan yana maka manuniya a kan har yanzu ba wani darasi da shugabannin kasar nan suka koya bare ya zame musu darasi.
Babu wasu shugabanni nagari da suka amsa sunansu da za su zauna su zuba idanu kasa irin kasar nan ta rinka kwangaba-kwanbaya da sunan wasu ba su tabuwa, da sunan ana mulkin dimokuradiyya. Dadin-dadawa ga al`amari ya kai fagen har kasarnan ta fada cikin yaki da `yan gwagwarmaya na `yan kungiyar Boko Haram, an fitar da kudi don sawo makamai, amma wasu su rabe tsakaninsu, don kawai wani ya ci gaba da zama akan karagar mulki.
Alhamdulillah cikin irin wannan mawuyacin hali da Gwamnatin Buhari ta samu kasar nan sai ga manyan kasashe duniya irin su Amurka da kasashen Turai da kungiyoyin su, irin su Majalisar dinkin duniya da kungiyar Tarayyar Turai da Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya, wato IMF da makamantansu, tun da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zaben 28 ga watan Maris din bara da bayan ya hau kan karagar mulki a cikin watan Mayun barar, suke ta ba shi tabbacin samun hadin kan su walau a daidaikun su ko a kungiya ce, a kan yadda zai yaki cin hanci da rashawa da samun dawo da dubun dubatar biliyoyin kudin kasar nan da irin wadancan mutane da suka rike madafun iko suka sace suka kai kasashen su. Tabbaci na baya-bayannan da Shugaba Buhari ya samu shi ne, daga Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wato UAE, Sheikh Muhammed Bin Zayad Al-Nahyan, mai Hedkwata a Dubai, Dubai din da a `yan shekarunnan ta zama babbar santar da shugabannin kasashe masu tasowa irin namu suke kai ajiyar kudaden da suka sata, bayan da tun a shekarun 1990, da kasashen Turai da Amurka suka rufe kofofinsu a kan shigar da haramtattun kudade.
Babu ko shakka waccan ziyarar kwanaki uku da Shugaba Buhari ya kai kasar ta Dubai, bisa ga wasu yarjeniyoyi da kasashen biyu suka rattafa hannu a kai, idan har an aiwatar da su sau da kafa, to, kuwa kasar nan za ta samu gagarumar nasara cikin gagarumin yakinta da ta daura da cin hanci da rashawa.
Kasancewar manyan kasar nan sun kwashe kudaden kasar nan sun kai kasar ta Dubai, ko dai sun sayi kaddarori irin su gidaje da filaye da kafa masana`antu da kamfanoni da sauran hanyoyin zuba jari, yayin da wasu suka ajiye tsabar kudin da suka sata a Bankunan kasar. Abin da ya sa na ce kasar nan za ta amfana, bai wuce daga cikin irin yadda a cikin yarjejeniyoyin da kasashe biyu suka sanya hannu akai har da wadda ta fayyace dalla-dalla cewa, daga yanzu dukkan mutanen kasashen biyu da a ka samu sun kwashe kudaden kasasu, sun kai kasar waccan kasa, to, kasar da aka kai kudaden za ta maido wa kasar da ke da kudaden, haka mutanen da suka aikata wani babban laifi, amma suka tsallake su shiga wata kasar, to, kasar da ya shiga din za ta taso keyarsa zuwa kasar ta sa. Hakazalika yarjejeniyar ta tanadi musayar `yan kurkukun kashen biyu, baya ga sauran yarjejeniyoyin da aka kulla akan inganta harkokinin kasuwanci da cinikayya da na masana`antu da zuba jari tsakanin kasashen biyu.
Ganin yadda kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawar ta karbi kasar nan, har aka cimma wannan yarjejeniya, ta sanya wasu mutanen kasar nan sun fara kiraye-kiraye ga Shugaba Buhari da sai ya kara haska fitilarsa zuwa kasashen gabas mai nisa, irin su Sin da Taiwan da Malesiya da sauransu, inda ake kyautata zaton `yan kasar nan sun kai kudaden da suka sata. Cin hanci da rashawa, mummunan alkaba`i ne da ya yake ruguza tattalin aarzikin kasa da ma zamantakewar mutanenta, don wasu na sace kudaden da za a yi wa `yan kasa ayyukan raya kasa, sannan kuma duk kasar da ta yi kaurin suna akan cin hanci da rashawa, shugabanninta da mutanenta da kasar kanta, ba su da mutunci da kima a idanun shugabannin duniya da mutanensa, musamman na kasashen da suka ci gaba.
Don haka wannan yaki ba yakin da Shugaba Buhari zai sassauta a kansa ba ne, wata barazana da cika baki daga irin wadanda ake zargi sun sace kudaden kasar nan bai kamata ta sa gwamnatin ta sassauta ba. Ya kuma kamata gwamnonin jihohi da shugabannin majalisun kananan hukumomin kasar nan su ma su fara na su yunkurin, ga sauran `yan kasa kuma su ci gaba da addu`o`i da kara yin hakuri.