Duk jami’in gwamnatina da ba zai zage dantse ba ya ajiye aikinsa — Tinubu

Tinubu ya gargadi ministocinsa su zage damtse don yin aiki tukuru.

Duk jami’in gwamnatina da ba zai zage dantse ba ya ajiye aikinsa — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce duk jami’an gwamnatinsa da ya nada dole ne su zage dantse su yi aiki tukuru don cimma muradun ’yan Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wajen bude taron kwana uku, wanda aka shirya wa ministoci, mataimakin shugaban kasa, da sauran jami’an gwamnati a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu, ya bayyana cewar dole ne a karshen taron a cimma matsaya tare da sanya hannu don gudanar da aikin gwamnatinsa kan ka’ida.

Don haka ya zaburar ministocinsa da sauran jami’an gwamnati da su taimaka masa don gwamnatinsa ta yi nasara.

Ya sake bayyana cewa a matsayinsa na dan Adam, zai iya yin kuskure, amma ya bukaci idan ya yi ba daidai ba a nusar da shi.

“Kuna matsayinku ne don taimaka min na yi nasara.”

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana cewa shi ne shugaban kasa ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da ko suna da alaka da jam’iyyun siyasa ba, ya ce zai dauki kowa a matsayin nasa.

“Na zo nan don ba da jagoranci ga wannan iyali don tabbatar da dangantaka mai karfi ta hanyar nuna kauna ga mutanenmu,” in ji shi.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, ya yi gargadin cewa bai kamata ma’aikatan gwamnati su kalli ministoci a matsayin wasu da za su zo su tafi ba.

Ya ce kamata ya yi a kalli ministocin a matsayin wasu mutane da za su bayar da gudummawa don ciyar da Najeriya gaba.

Tinubu ya ce ya karbi kadarori da bashin magabata, inda ya shaida wa mahalarta taron cewa, dole kowa ya shirya don magance kalubalen da ke gaban gwamnatin tasa.

Shugaban ya tabbatar wa ma’abota kasuwanci na kasashen waje cewa za su iya zuba jarinsu don samun riba ba tare da matsala ba.