Duk kilomita na layin dogon Abuja zuwa Kaduna sai da ya lashe biliyan daya

Wani bincike da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan daya da digo bakwai kwatankwacin Dala miliyan hudu da digo bakwai wajen gina kowace kilamita daya na aikin layin dogon Abuja zuwa Kaduna.   Binciken ya gano cewa layin dogon daga garin Abuja zuwa garin Kaduna ya kai jimillar […]

Duk kilomita na layin dogon Abuja zuwa Kaduna sai da ya lashe biliyan daya

Wani bincike da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan daya da digo bakwai kwatankwacin Dala miliyan hudu da digo bakwai wajen gina kowace kilamita daya na aikin layin dogon Abuja zuwa Kaduna.
 
Binciken ya gano cewa layin dogon daga garin Abuja zuwa garin Kaduna ya kai jimillar tsawon kilomita 186.
 
Binciken ya nuna cewa kudin da gwamnatin ta kashe ya fi  na kowane aikin layin dogo da aka gudanar da nahiyar Afirka tsada.