Duk lokacin da muka samu sabani da matata takan yi tsirara a gaban mutane – Magidanci
Wani magidanci mai suna Isiaka Adams, ya roki Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan ta raba aurensa da matarsa da suka shafe shekara 15 mai suna Bilkisu Adams saboda a cewarsa matar ba ta farin ciki da ci gaban da yake samu a wajen aikinsa. A cikin karar da ya shigar Isiaka […]
Wani magidanci mai suna Isiaka Adams, ya roki Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan ta raba aurensa da matarsa da suka shafe shekara 15 mai suna Bilkisu Adams saboda a cewarsa matar ba ta farin ciki da ci gaban da yake samu a wajen aikinsa. A cikin karar da ya shigar Isiaka Adams ya roki kotun ta dakatar da matarsa daga cin mutuncinsa da wulakanta shi a duk lokacin da aka samu sabani a tsakaninsa da ita. Ya shaida wa kotun cewa, “Wannan mata ba ta farin ciki da karin girman da na samu a wurin da nake aiki. Tana so a kore ni daga wannan aiki, shi ya sa take tasowa daga gidanmu ta zo har ofishin da nake aiki ta kama zagina tana fadin bakaken maganganu tare da tube suturartsa ta yi tsirara a gaban jama’a. Ta aikata haka a lokuta daban-daban.”
Ya ci gaba da shaida wa kotun cewa, “Bilkisu ta kasance mafadaciya da makwabtana sun isa shaida, na yi hakuri na tsawon lokaci tare da daukar matakan da suka dace domin gyara tsakaninmu amma ta ki dainawa. Saboda haka nake rokon kotu ta raba wannan aure na shekara 15. Raba wannan aure ne kadai zai sa in samu saukin rayuwa domin wurin da nake aiki sun sha gargadina a kan matsalar Bilkisu. Shi ne ya sa nake so a raba auren namu kafin ta kai ga hallaka ni.”
A yayin da kotun ta nemi jin ta bakin Bilkisu cewa ta yi “Ba na bukatar rabuwa da mijina domin ’ya’yanmu suna kanana a yanzu wanda rabuwarmu za ta iya jefa su cikin kunci da lalacewar rayuwa a nan gaba. Duk abin da mijina ya fadi karya yake shararawa.”
“Yanzu da yake samun ci gaba a wurin aikinsa ne yake son rabuwa da ni domin ya auro wata matar, shi ya sa yake yi mini kazafi. Tun da dadewa muke tare kuma za mu ci gaba da zama tare muddin ranmu,” inji ta.
Bayan sauraron bangarorin ne Shugaban Kotun Cif Ademola Odunade ya raba auren tare da bayar da umarnin ci gaba da rike ’ya’ya biyu na baya-baya masu shekara biyar zuwa tara a hannun Bilkisu, yayin da kotun ta umarci Isiaka Adams ya rike sauran yara uku da suka haifa da ita wadanda suka girma.
Kotun ta umarci Isiaka ya rika biyan Naira dubu 10 ga tsohuwar matarsa a kowane wata domin daukar dawainiyar karatu da lafiyar ’ya’yan nasu biyu.