Duk mai hannu a rikicin Kasuwar Magani zai dandana kudarsa-El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya umarci jami’an tsaro da su bincika tare da hukunta duk wanda ke da hannu a rikicin Kasuwar Magani. Gwamnan ya yi wannan sanarwar ca ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Samuel Aruwa. Aruwan ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi […]

Duk mai hannu a rikicin Kasuwar Magani zai dandana kudarsa-El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya umarci jami’an tsaro da su bincika tare da hukunta duk wanda ke da hannu a rikicin Kasuwar Magani.

Gwamnan ya yi wannan sanarwar ca ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Samuel Aruwa.

Aruwan ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da rikicin, sannan kuma tana jajantawa wadanda abin ya shafa.

Hakanan kuma gwamnatin ta umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da ta jihar da ta tantance wadanda rikici ya shafa tare da basu agaji cikin sauri.

Tuni dai aka tura jami’an tsaro yankin na Kasuwar Magani domin kare ci gaban rikicin.