Duk mai sukar gwamnatin Buhari azzalumi ne – Namaroko
Alhaji Hassan Umar Namaroko shi ne dan takarar Majalisar Dokikin Jihar Kebbi a mazabar Birnin Kebbi A, a Jam’iyyar APC a zaben 2019. A hirarsa da Aminiya a Birnin Kebbi ya ce duk mai sukar gwamnatin Buhari azzalumi ne: Wadansu ’yan Najeriya suna ta sukar gwamnatin Buhari me za ka ce a kan haka? Alhamdulillahi! […]
Alhaji Hassan Umar Namaroko shi ne dan takarar Majalisar Dokikin Jihar Kebbi a mazabar Birnin Kebbi A, a Jam’iyyar APC a zaben 2019. A hirarsa da Aminiya a Birnin Kebbi ya ce duk mai sukar gwamnatin Buhari azzalumi ne:
Wadansu ’yan Najeriya suna ta sukar gwamnatin Buhari me za ka ce a kan haka?
Alhamdulillahi! Na ji dadin wannan tambaya da ka fara yi min. Masu sukar gwamnatin Buhari ’yan adawa ne da masu hassada da azzaluman ma’aikata da barayin gwamnati da suka sace dukiyar jama’a da kuma wadanda ake satowa ana ba su suna cin banza.
Irin wadannan mutane ne suke sukar wannan gwamnati suke la’antarta, suna cewa wai ana cikin wani mawuyacin hali. A lokacin gwamnatin da ta gabata idan muka fito daga gidajenmu, muna ganin kamar ba za mu dawo ba saboda halin da ake ciki. Amma yanzu wannan tsoro ya kau sakamakon zuwan wannan gwamnati. A jihohin Arewa maso Gabas a baya noma da kiwon da muke yi Boko Haram sun hana. Duk inda mutum zai je a firgice yake duk ba mu ga wannan bala’i da Allah Ya kawar mana ba, shi ne ake cewa kasa ta shiga matsi?
Kuma mu a nan Jihar Kebbi mun ga babban canji mai ma’ana domin kananan manomanmu ba su taba samun nasarar noman rani irin shekara uku da suka gabata ba, saboda tallafawar da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kebbi suka yi. Saboda haka ina kira ga talakawan Najeriya su gane cewa masu wadannan sukar suna yi ne don bata wannan gwamnati. Kuma ina kira ga ’yan Najeriya mu ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’o’in alheri, mu yi watsi da masu wannan soki-burutsu.
Me kake gani a matsayin abin da ke taimakon Shugaba Buhari a wannan mulki?
A matsayina na Musulmi kuma Bahaushen Arewa, ina ganin babu abin da ya yi wa Shugaba Buhari garkuwa daga wani sharri sai shi wanda Ya dora shi kan wannan matsayi. Duk wanda ya san Buhari ya san mutum ne wanda yake tsare dokokin Allah. Buhari ba ya shan giya, ba ya neman matan banza, ba ya karya ko yaudara, ba ya munafunci. Mutum ne mai son ganin kowane lokaci an yi gaskiya an kuma yi adalci da sauransu. Allah Ya yi alkawarin duk bawan da ya tsare dokokinsa, zai kare wannan bawa da kariyarSa. Wannan ke nan! To amma sai kuma Allah Ya ci gaba da jarrabarsa a kan shugabancin da yake yi. Mu dubi irin yadda ake son ganin bayansa bisa wancan kudiri da niyyar mayar da Najeriya kyakkyawar turba tare da taimakon Allah, amma ba shi ne niyyar mafi yawan masu rike da mulki ba, ciki kuwa har da na jam’iyyarsa.
Wannan kai hari da ake yi masa ba a kan komai ba ne, illa wadansu sun zo domin su tara dukiya amma sai suka tarar hakan ba zai samu ba. Abin da Buhari yake da buri shi ne dan Najeriya ya san danta ne shi wanda zai yi alfahari da ita ta fuskar ci gaba da sauransu, sabanin yadda ake kallonmu a baya. Ya toshe duk wata hanyar da mutum daya zai kwashi kudin da ba shi ba, ko jikokinsa sai sun yi shekaru kafin su kashe su.
Yaya kake ganin irin su?
Ai duk masu kwasar kudin nan suna kaiwa kasashen waje don boyewa dama can masu mugunta ne. Ai kamata ya yi koda sun kwashi kudin, to, su kafa kamfanoni da masana’antu a cikin gida mana, ta yadda za su tallafa wa rayuwar wadansu kila ko ta nan an dan rage wani abu na alhakin da aka dauka. Karshe ma in mutum ya mutu shi ke nan ya yi wa hatta ’ya’yan da ake takama da su bakin ciki, saboda ba za su amfana da su ba.
Ke nan ka goyi bayan yaki da cin hanci da rashawar da ake yi?
Ai ba ni kadai ba, duk dan kasa nagari yana goyon baya. Ya kuma zama wajibi a yi yaki da cin hanci a kasar nan in dai muna so mu ci gaba. Ko ba komai mun ga fa’idar wannan yaki da cin hanci tunda ya tona asirin mutanenmu na boye wadanda suka yi rub-da-ciki da dukiyarmu.
Ana korafin cewa Shugaba Buhari ba ya daukar shawara, me za ka ce?
Batun cewa Buhari ba ya daukar shawara abin yana daure mini kai. Wadansu na cewa haka yayin da wadansu kuma ke cewa, na kusa da shi ne suke hana ruwa gudu saboda sun dabaibaye komai, sai abin da suka ce. To in ma har haka ne ashe Buhari na daukar shawara, saboda na kusa da shi din ai shawara suke bashi ayi kaza ko a bar kaza. Ka ga maganar ana yin tubka da warwara ke nan.