Duk mai yakar gwamnatin Buhari bai kaunar Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’iah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce duk wanda yake yakar gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, ba mai kaunar Najeriya da al’ummarta ba ne. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida, kan rikicin […]

Duk mai yakar gwamnatin Buhari bai kaunar Najeriya – Sheikh Jingir
Duk mai yakar gwamnatin Buhari bai kaunar Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’iah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce duk wanda yake yakar gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, ba mai kaunar Najeriya da al’ummarta ba ne. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida, kan rikicin da ya faru tsakanin ’yan Shi’a da sojoji a Zariya da yunkurin ballewa daga Najeriya da al’ummar Ibo suke yi.

Ya ce duk wani dan Najeriya mai kishi, ya san irin mummunan halin da kasar nan ta shiga a baya, kuma ya fito ya yi addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan mummunan hali. Kuma Allah Ya amshi addu’ar ’yan Najeriya ta hanyar kawo Shugaba  Buhari. Ya ce don haka duk wanda zai zo yanzu yana yakar wannan gwamnati, to ba mai kaunar kasar nan ba ne.
Ya ce abubuwan da ’yan Shi’a suke yi na tare hanyoyi idan suna gudanar da tarurrukansu, ya saba wa addinin Musulunci kuma ya saba wa dokokin Najeriya. “Duk lokacin da wani mutum ya toshe wata babbar hanya da mutane suke bi, a yi kamar awoyi biyar ana jira kafin a samu a wuce bai dace ba, domin an cutar da jama’a. Kuma wannan abu na tare hanyoyi da ’yan Shi’a suke yi, an yi shekaru da dama ana gudanar da shi,” inji shi.
Ya ce akidarsu ta zagin matan Manzon Allah (SAW) da sahabbansa ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba. Don haka ya ce kungiyar Izala ta yi shekaru tana kira ga gwamnati kan ta lura da abubuwan da ’yan shi’a suke yi a Najeriya.
Malamin ya yaba wa matakin da gwamnonin Arewa suka dauka, na cewa ba su yarda a rika tsare hanyoyi ba, a lokacin da wata kungiyar addini ke gudanar da harkokinta. Da kuma cewa dole duk wani da zai yi wani taro ya sanar da hukuma, don ya samu izini. Ya ce: “Muna goyon bayan gwamnoni kan wannan mataki da suka dauka.”
Da ya juya ga masu yunkurin kafa kasar Biyafara, Sheikh Jingir ya ce kungiyar Izala ta yi Allah wadai da wannan yunkuri na ballewa daga kasar nan. Daga nan ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye don magance matsalar man fetur da ake fama da shi a kasar nan a yanzu. Ya ce matsalar karancin man fetur ta jefa al’ummar kasar nan a cikin mawuyacin hali; don haka gwamnati ta taimaka ta magance ta.