Duk malamin da ya shiga yajin aiki zai rasa aikinsa – El-Rufa’i

A yayinda malaman makaranta suka shiga tsunduma cikin yajin aiki a Jihar Kaduna, Gwamnar jihar, Nasir El-Rufa’i ya ce duk wani malami da ya ki zuwa aiki zai rasa aikinsa. A cewarsa, gwamnatin za ta dauki matakin korar duk wani malami da bai shiga aji ya koyar da dalibai ba. A ranar Litinin da ta […]

Duk malamin da ya shiga yajin aiki zai rasa aikinsa – El-Rufa’i

A yayinda malaman makaranta suka shiga tsunduma cikin yajin aiki a Jihar Kaduna, Gwamnar jihar, Nasir El-Rufa’i ya ce duk wani malami da ya ki zuwa aiki zai rasa aikinsa.

A cewarsa, gwamnatin za ta dauki matakin korar duk wani malami da bai shiga aji ya koyar da dalibai ba.

A ranar Litinin da ta gabata ce kungiyar Malaman Makaranta ta umurci ’ya’yanta da kada su koma makaranta domin karantar da ddalibai har sai gwamnatin ta janye shirinta na korar malaman firamare 22,000 daga aiki.

Idan ba a mance ba, Gwamnatin Jihar ta ba da umurnin korar malaman firamare 22,000 wadanda suka fadi jarabawar gwaji ta ’yan aji hudu da aka yi masu. Wannan mataki na gwamnatin jihar ya samu tirjiya daga kungiyar malaman da kuma kungiyar kwadigo da kuma wasu jama’a a jihar.

Sai dai gwamnatin jihar a wata sanarwa da ta fitar dangane da yajin aikin da malaman suka shiga, mai dauke da sa hannun Kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan, ta ce a shirye take ta kori duk malamin makarantar da ya ki komawa bakin aikinsa.

“Labari ya zo mana cewa wai kungiyar Malaman Makaranta ta fara yajin aiki, wannan ya sa muke kira da yin gargadi gare su cewa duk malamin da ya ki komawa bakin aiki domin ci gaba da karantar da yara, zai rasa aikinsa.

“Gwamnati ba za ta zura ido wasu ’yan tsiraru su mayar mata da hannun agogo baya ba. Ba za mu yi wasa da rayuwar yara sama da miliyan biyu ba, don haka wannan yajin aiki ba zai hana mu ci gaba da gyaran da muke son yi a sashen ilimi ba,” inji shi.

Rahotanni sun nuna cewa makarantu da dana a cikin garin Kaduna sun kasance kamar an share su, duk kuwa da gargadin na gwamnatin jihar, inda dalibai suka kasance a gidajensu.

Amma a ranar Talatar da ta gabata, akwai malamai da suka fito bakin aiki a wasu makarantun amma ba su shiga aji ba. Su kuma daliban wasu sai kwallo da guje-guje kawai suke yi cikin makaranta.

kokarin jin ta bakin shugaban kungiyar malaman na jiha, Adamu Zango ya ci tura, domin wayarsa a kashe take.