Duk maniyyatan da suka biya kudi a Filato za su tafi aikin Hajji – Sheikh Jingir

Amirul Hajji na Jihar Filato kuma Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce da yardar Allah duk maniyyacin da ya biya kudin kujerar aikin Hajjin bana a Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, zai tafi. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne […]

Duk maniyyatan da suka biya kudi a Filato za su tafi aikin Hajji – Sheikh Jingir
Duk maniyyatan da suka biya kudi a Filato za su tafi aikin Hajji – Sheikh Jingir

Amirul Hajji na Jihar Filato kuma Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce da yardar Allah duk maniyyacin da ya biya kudin kujerar aikin Hajjin bana a Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, zai tafi.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, bayan da ya kai ziyara ofishin Hukumar Alhazai ta Jihar da ke Jos.
Ya ce “Da yardar Allah a aikin Hajjin bana za mu yi iyakar kokarinmu wajen ganin ba a bar wani maniyyaci da ya biya kudin kujerar a jihar a gida ba, kamar yadda ya rika faruwa a baya.”
Sheikh Jingir ya ce a ziyarar da ya kai ofishin hukumar ya ga irin varnar da jami’an gwamnatin jihar da ta gabata suka tafka, inda suka cinye kudin ajiyar maniyyata har Naira miliyan 300.
Ya yi kira ga Gwamna Simon Lalong kan ya matsa wa wadanda suka wawushe kudin domin su dawo da su. Kuma ya yi kira ga maniyyatan jihar Filato su yi shirin karantar yadda ake aikin Hajji da kuma  na guzuri kuma su kasance masu hakuri da juriya a lokacin aikin Hajjin.
A makon jiya ne Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya amince da nadin Sheikh Sani Yahya Jingir a matsayin Amirul Hajji na bana, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga Daraktan Labarai na Gwamnan, Mista Samuel Emmanuel Nanle ta bayyana.