Duk tsokar da ta ginu da haram wuta ce makomarta! (3)

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya Fassarar Salihu Makera Ciniki a kan cinikin wani: Kuma daga cikin dukiyar haram, akwai yin ciniki a kan cinikin wani ko mutum ya sayar da kaya ga wani bayan ya sayar ga wani. Kamar mutum ya sayar wa wani kaya sai ya kai talla ga wani a kara masa kudi ya sayar, […]

Duk tsokar da ta ginu da haram wuta ce makomarta! (3)

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya

Fassarar Salihu Makera

Ciniki a kan cinikin wani: Kuma daga cikin dukiyar haram, akwai yin ciniki a kan cinikin wani ko mutum ya sayar da kaya ga wani bayan ya sayar ga wani. Kamar mutum ya sayar wa wani kaya sai ya kai talla ga wani a kara masa kudi ya sayar, ya yi hakan da niyyar cutarwa ce ko ba da niyya ba, wannan saye da sayarwa haram ne. Haka cinikin wani Musulmi a kan cinikin dan uwansa. Kamar wani ya sayi kaya a wurin wani, sai wani mai saye ya zo ya saya domin ya bata cinikin na farko da niyya ya yi ko ba da niyya ba, wannan ciniki haram ne. Saboda fadinsa (SAW): “Kada dayanku ya yi ciniki a kan cinikin dan uwansa har sai ya gama cinikin ya saya ko ya fasa.” Muttafakun alaihi, amma lafazin na Nisa’i ne.

Don haka ba ya halatta ga wani Musulmi idan ya ga dan uwansa ya taya kaya ya je ya kama tayawa, har sai wancan ya gama saye ko ya fasa saye. Haka ba ya halatta ga Musulmi ya sayar da kayan da wani ya saya ga wani daban, har sai wancan ya gama saya ko ya hakura. Haka ba ya halatta wani ya yi tayi a kan tayin dan uwansa.

Wadannan suna daga cikin kyawawan halayen Musulunci da kyawawan dabi’unsa abin godiya da siffofinsa madaukaka,  wadanda ’yan kasuwa da dama a yau suka rasa su, musamman a wajen saye da sayarwarsu. 

Ina horonku da jin tsoron Allah da guje wa nema ko cin dukiyar haram, domin  Allah Mai tsarki ne kuma ba Ya karbar aiki sai mai tsarki.

Ku guji abubuwa masu kawo fushin Allah, ku ci halal mai dadi domin Allah Ya sanya albarka a cikin abin Ya azurta ku.


Algushu

Kuma daga cikin cin dukiyar haram, akwai yin algushu da boye aibi ga mutane a cikin mu’amaloli, ta yin haka sai a ci dukiyar mutane da karya. Wato kamar mutum ya sanya abu mai kyau a saman marar kyau, ko ya sanya sabo a kan tsoho ko irin yadda masu kasa doya da dankali da tumatir da sauransu suke yi, su sanya manya a sama su lullube kanana a kasa. Duk wadannan abubuwa ba su halatta ba a shari’a. Kuma hakan yana daga cikin algushun da mutane suke yawan aikatawa a yau.

An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya wuce ta wurin wani garin abinci sai ya sanya hannu a ciki sai yatsunsa suka jike. Sai ya ce: “Mene ne haka ya kai mai wannan abinci?” Sai ya ce: “Ruwan sama ne ya doke shi ya Manzon Allah!” Sai ya ce: “Don me ba ka sanya jikakken a sama ba, ta yadda mutane za su gani? To duk wanda ya yi mana algushu ba ya tare da ni.” Muslim ya ruwaito.

Ina Musuluncin kuma ina ’yan uwantakar da Littafin Allah ke cusa mana kuma Manzon Allah (SAW) ke umartarmu da ita? Shin mutane ba za su ji tsoron Allah su san gaskiya su bi ta ba, kuma su san halal su amfana da ita ba, kuma su san haram su guje mata ba?

Domin  haka ku ji tsoron Allah ya ku ’yan kasuwa! Ku rika bayyana aibin kaya ga mutane kafin sayar da shi, Allah ne Mai azurtawa kuma Shi Ma’abucin karfi ne tabbatacce.

An karbo daga Ukbatu bin Amir (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Musulmi dan uwan Musulmi ne, ba ya halatta ya sayar wa dan uwansa kayan da yake da aibu face ya bayyana masa.” Ibn Majah da Ahmad suka ruwaito. Kuma an karbo daga Wa’ilah bin Al-Ash’as (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wanda ya sayar da kaya mai aibu kuma bai bayyana shi (aibun) ba, ba zai gushe ba yana cikin fushin Allah, kuma mala’iku za su yi ta la’antarsa.” Ibn Majah ya ruwaito.

Don haka duk wanda ya san akwai aibu a cikin kayansa wajibi ne a kansa ya bayyana aibun ga mai saye, domin wannan hakkin Musulmi ne a kan dan uwansa, kuma ba ya halatta gare shi ya boye masa, idan ya boye masa ya yi laifi.

Haka haram ne mutum a aike shi sayen kaya su hada kai da mai sayar da kayan a sayar masa kan kudi daban da ainihin kudin da zai bayyana ga wanda ya aike shi sayo kayan. Haka haram ne mutum ya sayar da kayan da ya san jabu ne a kan mai kyau ga wani mai saye. Dukan wadannan hanyoyi ne na cin dukiyar haram, kuma duk wanda ya ci su, ya ci wuta, don haka mutum ya ji tsoron Allah ya guji haka  ko ya hadu da nadama!


Kayan Kade-Kade:

Haka daga cikin dukiyar haram akwai dukiyar da ake samu ta hanyar sayar da kayan da suke cakude da haramci kamar kayayyakin kade-kade da wake-wake, kaset-kaset da suke dauke da alfasha da cin zarafin Musulmi ko bata wasu dabi’un Musulunci ko cin zarafin malamai da shugabannin Musulunci da sauran maganganu na cin zarafin addinin Musulunci. Sayar da ganguna da kaset din wakoki na rediyo da na bidiyo da fina-finan da suke bata tarbiyya suke kaiwa ga aikata haram da kangewa daga tafarkin Allah da nesanta mutane daga hanya madaidaiciya da kuma ambaton Allah duk sun shiga karkashin wannan babi.


Giya da Kayan Maye:

Haka daga cikin dukiyoyin haram akwai sayar da giya ko dakonta ko tallafa a sana’anta ta ko sayar da taba da wiwi da hodar Iblis da kwaya da sauran kayayyakin sanya maye, wadanda cutarwarsu ba su boyuwa ga kowane Musulmi daidaikunsu da a kungiyancensu da kuma kasashensu.

Lallai idan Allah Madaukaki Ya haramta wani abu, to Ya haramta cin kudinsa. Don haka wadannan kudade da ake samu ta hanyar sayar da abubuwan da suke lalata rayuwar matasan wannan al’umma maza da mata, haram ne mafi munin haramci. Duk mai sayar da kayan maye yana jefa kansa ne a cikin ukuba – muna neman tsarin Allah- idan aka sanya shi a cikin kabarinsa da kuma lokacin da zai hadu da Ubangijinsa. Wadannan dukiyoyi da aka samu ta wadannan hanyoyi da muka ambata da wadanda ma ba mu ambata ba, amma sun yi kama, ba halal ba ne, cin su haramun ne, kuma duk jiki ko tsoka da ta yi kitse da irin wannan dukiya wuta ce ta fi dacewa da shi, Allah Ya yi mana tsari.

Don haka ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi! Ku sani abin sani wannan rayuwa ta duniya ’yan kwanaki ne kadan, kafin ka zauna ka kintsa sai ka ga lokaci ya kure ka tafi Lahira. Kwatsam sai mutum ya iske kansa a tsaye a gaban Allah Mai tsananin karfi – TsarkinSa ya tabbata- kuma Ya tambaye shi daga dukiyarsa: Ta ina ya same ta? Kuma yaya ya kashe ta? Ubangijinsa zai tambaye shi – alhali Shi ne Mafi sani game da shi- Yaya ya yi da umarce-umarcen Alkur’ani da Sunnah da kuma hane-hanensu. Shin ya yi da’a ga umarce-umarcen kuma ya hanu daga hane-hanen ko kuwa ya aikata haramce-haramcen kuma ya bar halal?

Don haka ya ku mutane! Ku shirya amsoshin da za ku bayar ga tambayoyin da za a yi muku. Kuma ku tabbatar amsoshin sun dace da abin da Allah Ya yi umarni. Babu makawa tilas ne a ji tsoron Allah a cikin mu’amaloli, a ji tsoronSa a boye da bayyane, a ji tsoron Allah Madaukaki Wanda Shi Masanin sirrori da abin da zukata suka boye ne, kamar yadda yake sanin ha’ince-ha’incen idanuwa da abin da kiraza suke boyewa. 

Allah ne Mai ida nufi, kuma Shi ne Mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a kan Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.