Duk wanda aka kama da katin zabe na bogi zai gurfana gaban kotu – Zarewa
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce an dauki kwararan matakai don magance magudi a zaben da ke tafe a karshen watan gobe. Kwamishinan Hukumar a Jihar Kebbi Alhaji Aji Jibrin Zarewa ya bayyana haka, inda ya ce duk mai kada kuri’a da aka kama shi da katin zabe na bogi zai gurfana a gaban […]
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce an dauki kwararan matakai don magance magudi a zaben da ke tafe a karshen watan gobe.
Kwamishinan Hukumar a Jihar Kebbi Alhaji Aji Jibrin Zarewa ya bayyana haka, inda ya ce duk mai kada kuri’a da aka kama shi da katin zabe na bogi zai gurfana a gaban kotu.
Alhaji Jibrin Zarewa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, inda ya ce Hukumar INEC ba za ta lamunci kowane nau’i na magudi ba a zaben da za a yi, kuma ya ce duk wani mai kada kuri’a da yake tunanin zai yi zabe da katin bogi ko na wani ya yi wa kansa kiyamullaili ya bari, idan ba haka ba zai tsinci kansa garkame a gidan yari.
Kwamishinan ya ce hukumar ta yi tanadi sosai don hana masu magudin zabe cin karensu babu babbaka, don haka magudin zabe ya zama tarihi a Najeriya.
Idan za a tuna an sanya ranar 28 ga Maris mai zuwa domin gudanar da zaben Shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa, sai ranar 11 ga Afrilun a matsayin ranar zaben gwamnonin da ’yan majalisun dokoki na jihohi.