Duk wanda ya ce shugaba ba zai yi sha’awar wanda zai gaje shi ba, ba Musulmi ba ne – Gwamnan Neja
Jam’iyyar PDP a Jihar Neja ta kama hanyar fadawa cikin rikicin da in ba a dauki mataki ba, na iya jawo mata matsala a zabe mai zuwa. Wannan ya biyo bayan matsayin da Gwamnan Jihar Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya dauka ne na fitowa fili ya ce yana goyon bayan Alhaji Umar Muhammad Nasko a […]
Jam’iyyar PDP a Jihar Neja ta kama hanyar fadawa cikin rikicin da in ba a dauki mataki ba, na iya jawo mata matsala a zabe mai zuwa. Wannan ya biyo bayan matsayin da Gwamnan Jihar Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya dauka ne na fitowa fili ya ce yana goyon bayan Alhaji Umar Muhammad Nasko a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar.
Gwamna Babangida ya ce duk wata tawaga daga shiyya ta uku da ta zo masa da kokon bara daga sauran ’yan jam’iyyar da suka nuna sha’awar takarar a gaya musu su janye, kuma wanda ya ki, idan aka je wurin daga zai gani a kwaryarsa.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Duk wanda ya ce, shugaba ba zai yi sha’awar wanda zai gaje shi ba, ba Musulmi ba ne. Haka kuma duk wanda ya ce bai kamata ina da dan takara ba, maganar banza ce. Ina kuma gaya wa mutane su fahimci cewa maganar da ake cikin gari cewa Umar Muhammad Nasko yana da karancin shekaru, don haka bai kamata ya zama Gwamna ba, su binciki tarihin jihar za su ga cewa akwai tsofaffin gwamnonin jihar da suka shugabanci jihar ba su kai shekara 40 ba.”
Da yake jawabi, Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Neja wanda ya yi magana a madadin Majalisar kolinta ya shaida wa wadanda suka ziyarci Gwamnan cewa suna mara wa Alhaji Umar Muhammad Nasko baya kuma za su yi duk abin da ya kamata don ganin cewa an cimma burin da aka sa a gaba tare da samun gagarumar nasara a zaben badi.
Dukkan wadanda suka yi jawabi a wurin ziyarar sun bayyana gamsuwarsu kan yadda Gwamna Babangida Aliyu ya gudanar da ayyukan raya yankin duk da cewa shiyyar ta fada a hannun jam’iyyar adawa. Sun ce wannan ne babban dalilin da ya sa suka nemi ya ba su Alhaji Umar Muhammad Nasko a matsayin wanda zai gaje shi, su kuma za su yi masa kamfe.
daya daga cikin wadanda suke sha’awar jam’iyya ta tsayar da su takararar Gwamna Alhaji Saleh Sahabi darangi ya shaida wa wakilinmu cewa wadanda suka kai wa Gwamna wannan tayin ba fitattun ’yan siyasar shiyya ta uku ba ne, magoya bayan Alhaji Umar Nasko ne da aka yi hayarsu domin biyan bukatar wanda suka nemi Gwamnan ya mara wa baya don ya gaje shi.