Duk wanda ya gode wa ni’imar Allah zai samu kari (4)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni’imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya ce duk wanda ya gode wa ni’imarSa, zai samu kari. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau za mu ci gaba da mukalar tamu ne daga bayanin:
Falalar godiya da yabon gamsuwa ga Allah
Allah Ta’ala Ya ce, “To, ku ambace (tuna) Ni, In tuna (ambace) ku, kuma ku yi godiya gare Ni (ku gode miNi), kada ku butulce (kafirce) miNi.” Surar Bakarah, aya ta 152. Ibnu Jarir Addabari ya ce, ma’anarta ita ce, ‘Ku ambace Ni ya ku muminai, ta hanyar biyayya a gare Ni, cikin abin da Na umarce ku, ta hanyar yi muku rahama da gafarta muku kura-kuranku, kuma ku gode miNi game da ni’imar da Na yi muku ta Musulunci da shiryuwa zuwa ga addinin da Na shar’anta muku, kada ku kafirce wa kyautatawar da Na yi muku, domin Zan iya kwace ni’imar da Na yi muku.’
An karbo daga Suhaib (Allah Ya yarda da shi), ya ce, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ina mamakin al’amarin mumini, lallai al’amarinsa gaba dayansa alheri ne, hakan ba ya tabbata ga kowa, sai ga mumini. Idan (abin) farin ciki ya same shi, sai ya yi godiya, sai ta zama alheri gare shi; idan abu mai cutarwa ya same shi, sai ya yi hakuri, sai hakan ya zama alheri gare shi.” Imam Muslim, Hadisi na 2,999.
Haka nan Allah (Subhanahu Wa Ta’ala), Ya ce, “Kuma ka ce, “Godiya ta tabbata ga Allah….” Surar Isra’i, aya ta 111. Sannan Allah Ya ce (game da wadanda suka yi imani, suka aikata ayyukan kwarai, aka shigar da su cikin gidajen Aljannar ni’ima, sai ya kasance karshen kiransu a cikinta), “…Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halitta.” Surar Yunus, aya ta 10.
Falalar da ke kunshe a cikin godiya da yabon gamsuwa ga Allah ba ta kididdiguwa, domin da ita (godiyar, tunda an yi imani da Allah da abin da aka aiko ManzonSa da shi aka yi ayyukan kwarai) ake samun gidan Aljanna, wurin da ake da wata irin ni’imar da ido bai taba ganin irinta ba, zuciya ba ta taba darsuwa game da irinta ba, kuma kunne bai taba jin labarin irinta ba.
An samo daga Abu Musa Al Ash’ariy (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah, (Sallalahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Idan dan bawa ya mutu, sai Allah Ta’ala Ya ce wa Mala’iku (alhali Yana sane), “Kun dauki ran dan bawaNa?’ Sai su ce, “Na’am.” Sai kuma Ya (sake) cewa, “Yanzu kun karbi ran daya daga cikin sanyin idonsa.” Sai su (sake) cewa, “Na’am.” Sai Ya ce, “To me bawaNa ya ce?” Sai su ce, “Ya gode maKa (ya nuna gamsuwarsa kan abin da Ka kaddara masa), kuma ya yi istirja’i (wato ya fadi kalmar ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un’- daga Allah muke, kuma gare Shi ake mayar da mu).” Sai Allah Mai girma da daukaka, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, Ya ce, “Ku gina wa bawaNa wani gida a Aljanna, kuma ku sanya wa gidan suna “Baitul Hamdi” (wato gidan godiya).” Imamu Tirmizi ne ya ruwaito Hadisin kuma ya ce hasanun ne.
Yaya zan gode wa ni’imar Allah?
Daga abin da ya gabata, mun karanci yadda godiya take da muhimmanci da falala da kuma riba a nan duniya da kuma a Lahira. Kowane irin abu da Allah Ya nuna farin cikinsa game da shi, lallai yana da muhimmanci. Duk abin da mutum ya samu karuwa a kansa, lallai yana da falala, kuma zai ga ribarsa ninki-ninki, musamman a gidan da ba a mutuwa, ashe wannan abu yana da babban matsayin da ya kamata lallai ya maida hankali a kan rike shi da nagarta.
Yadda za a gode wa Allah kuwa ya kasu uku: (1) Ana gode wa ni’imar Allah da zuciya; (2) Ana godiya da baki; sannan (3) Ana godiya da gabban jiki.
(1) Shi nuna godiya da zuciya yana da alaka ne da sadar da samuwar ni’imar ga Wanda Yake bayar da ita, wato mutum ya hakkake a zuciyarsa cewa lallai babu wani da ya isa ya bayar da wannan ni’ima (kowace iri ce), sai Mai ita, Allah (Subhanahu Wa Ta’ala), Shi kadai! Duk ta inda ko yadda mutum ya samu wani alheri, sai dai (ta inda ko yadda din) ya zama sila (dalili), amma ba shi ne ke bayar da alherin ba. Wannan kuwa haka ne, kamar yadda Allah Madaukaki (bayan Ya nuna isarSa a kan duk abin da ke cikin sammai da kassai, cewa kowa da komai gare Shi yake rusunawa), sai Ya ce, “Kuma duk abin da yake a gare ku na ni’ima, to daga Allah ne.” Suratun Nahli, aya ta 53.
(2) Kuma nuna godiya da harshe yana da alaka ne da yawaita furta yabon abin da aka samu na ni’ima din ga Wanda Ya bayar da ita, domin godiya ita ce tsororuwar yabo kuma farkonsa, kuma yana daga cikin mafi darajar abin da harshe yake motsawa ya furta shi. Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), ya ce, “….Kuma alhamdulillahi, wato fadin godiya ta tabbata ga Allah, tana cika mizanin awon kyawawan ayyuka…” Imam Muslim ne ya ruwaito Hadisin.
(3) Nuna godiya da gabbai kuwa shi ne yin aiki da su wajen tsayuwa da ayyukan alheri kyawawa kan samun yardar Allah da kuma hanuwa daga aiwatar da su wajen saba wa Allah da fadawa cikin wuraren da za a zame daga kyakkyawan tafarki. Mafi daukaka daga cikin halittar Allah shi ne wanda ya sanya ni’ima da sauran abubuwan da Allah ke kwararowa na alheri zuwa ga neman yardar Allah da samun gidan Lahira. Mafi kaskancinsu kuwa shi ne wanda ya karkatar da ni’imarsa zuwa ga bin son zuciyarsa da duk abin da zai jiyar da shi dadi na garari.
Saboda haka sai ka kasance (mai kana’a) wato mai wadatuwa da abin da Allah Ya azurta ka da shi, don ka kasance mafi godiyar mutane. Kuma ka rika tuna cewa godiya da gamsuwa da ni’imar Allah, ibada ne daga cikin mafi daukakarta domin Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wanda aka ciyar da abinci ya gode, kamar mai azumi ne mai hakuri.” Imamu Buhari ne ya fitar da Hadisin.
Allah Ya sanya mu cikin masu godiya kan ni’imar da Ya yi mana don girman zatinSa da karimcinSa da tsarkin sunayenSa, amin!
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!