Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas
Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu
Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha.
Babban Sakatare a ofishin da ke kula da magudanun ruwa da tsaftar ruwan sha a jihar, Mahmood Adegbite ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ruwan sha a jihar a kwanakin baya.
- DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?
- ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’
Mahmood ya kuma ce gurbataccen ruwan sha a unguwar zai iya haifar da barazanar lafiya matukar ba a bi hanyoyin da suka dace wajen tsaftace shi ba.
Ya ce, “Game da batun kula da tsaftar muhalli kuwa, zan iya cewa duk wanda ya haka burtsatse a yankin unguwar Lekki, watakila yana shan ruwan da zan iya kira da ruwan masai ne.
“Amma idan muka yi kokari wajen sarrafa dattin da yake fitowa daga yankin kamar yadda muke yunkurin yi a yanzu haka, za mu dakile duk wata cuta da za ta iya yaduwa sanadiyyar rashin tsafta,” in ji shi.
Sai dai ya ce akwai jan aiki a gaban jihar wajen magance matsalar ambaliyar ruwa, yana mai cewa ko a watan da ya gabata sai da aka samu ambaliyar a wasu sassan jihar, sabanin a watan Agustan da aka saba gani a shekarun baya.
“Maganar gaskiya a bangaren ambaliya, duk da muna namijin kokari wajen magance ta, amma har yanzu akwai jan aiki a gabanmu kafin mu iya magance matsalar baki daya,” in ji Babban Sakataren.