Duk wanda ya muzanta Manzon Allah kafiri ne – Sheikh dahiru Bauchi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a darikar Tijjaniyya Sheikh dahiru Usman Bauchi ya wanke darikar Tijjaniyya daga batancin da wani mai suna Abdul Inyas ya yi ga Annabi Muhammad (SAW) a lokacin Maulidin Nyass a birnin Kano, inda ya ce duk wanda ya muzanta Annabi (SAW) kafiri ne. A wata tattaunawa da ya […]

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a darikar Tijjaniyya Sheikh dahiru Usman Bauchi ya wanke darikar Tijjaniyya daga batancin da wani mai suna Abdul Inyas ya yi ga Annabi Muhammad (SAW) a lokacin Maulidin Nyass a birnin Kano, inda ya ce duk wanda ya muzanta Annabi (SAW) kafiri ne.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa jiya alhamis, an ruwaito Shehun Malamin yana cewa: “Shi Shehu ma ai saboda girmama Manzon Allah (SAW) ne ya sa Allah Ya girmama shi. Duk wanda ba ya ganin girman Manzon Allah (SAW) kafiri ne. Wadannan bakaken maganganun ba na Musulmi ba ne. Duk wanda bai ganin girman Manzon Allah (SAW) komai girmansa kafiri ne. Ba ruwanmu da su wadannan mutane masu maganganun banza kuma ba ’yan Tijjaniyya ba ne.”
Sheikh dahiru Bauchi ya ce: “Kwankin baya mun sa ’yan sanda sun kama mana wani kafiri me cewa Shehu wai bai haihu ba, ba a haife shi ba. Shehu ga ’ya’yansa muna gani, a ce bai haihu ba? Shehu ga iyayensa yana rubutawa, sunan mahaifinsa Abdullahi Inyas. Kuma in da haka ne bayaninsa, ba a haife shi ba, me ya sa ya rasu? Ba ruwanmu da su.”
Sheikh dahiru Bauchi ya kara da cewa, masu irin wadannan maganganu na batanci, ba ’yan Tijjaniyya ba ne wasu ne da suke kiran kansu Ahlul Hakika, don haka babu ruwan Tijjaniyya da su.
Ya kara da cewa, ’yan hakika ba ’yan Tijjaniyya ba ne, “Duk wanda ya ce haram halal ne, kafiri ne, ba ya darikar kowa. Duk wanda ya ce ya yi tarbiyya ya gano haram halal ne ya yi ridda ya karyata Alkur’ani ya karyata Sunnar Manzon Allah (SAW),” inji shi.
Sheikh dahiru Bauchi ya ce Tijjaniyya ba ta cewa kaza haram ne ko kaza halal, duk abin da yake haram ne a Musulunci, haram ne a wurin ’yan Tijjaniyya, haka ma halal. Ya ce: “Ba mu da wani bambanci a tsakaninmu da sauran Musulmi sai dai Lazimi da Wazifa da Zikirin Juma’a da muka dauki alkawari kuma Allah Ya ce: “Ku cika alkawari, lallai ne alkawari ya kasance abin tambaya.”
Shi ma jagoran darikar Tijjaniyya a Kano, Khalifa Isiyaka Rabi’u ne ya barrantar da mabiya darikar inda ya ce babu ruwan darikarsu da duk wanda ya fito ya fadi wasu kalamai da suka saba wa shari’ar Musulunci. “Muna sanar da jama’a cewa duk wanda aka samu yana aikatawa ko furta wata magana da ta saba wa shari’ar Musulunci ba masoyin Shehu Ibrahim Nyass ba ne, domin har Shehu Nyass ya bar duniya bai daina azumi ko Sallah ko Hajji ba, haka ma halifofin da suka biyo bayansa.”
Khalifan na Tijjaniyya ya kara da cewa “A matsayinmu na shugabanni ba za mu zura ido mu kyale wasu batagari su rika amfani da sunan Shehu Ibrahim suna aibata Annabi Muhammad (SAW) ba.”
Ya ce suna tattaunawa da sauran shugabannin Majalisar Shura ta darikar Tijjaniya da kuma hukuma don daukar mataki a kan wadannan miyagun mutane. Sai ya yi kira ga jama’ar Musulmi su kwantar da hankalinsu tare da yin biyayya ga shugabanni.
Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa ma, ya bayyana wannan lamari a matsayin abin da hukumarsu ba za ta amince da shi ba, kuma ba za ta saurara ba har sai ta gurfanar da mutumin gaban kotu. “Hukumar Hisba ba za ta amince da irin wadannan mutane su ci gaba da yin wannan katobara ba. Yanzu haka mun fara tuntubar lauyoyinmu don ganin mun gurfanar da wannan mutum a gaban kotu,” inji shi.
A wani labarin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da mutum uku a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo a birnin Kano da ake zargi da hannu a shirya Maulidin da aka yi kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Mutanen da suka hada da Mairo Ibrahim da aka fi sani da Mairon AC da danjummai Muhamamd da Aminu Muhammad sai kuma wasu mutum hudu da ’yan sanda ke nema ciki har da wanda ake zargi da kalaman batancin wato Abdul Nyass.
’Yan sanda sun kama mutanen ne sakamakon kalaman batancin da suka yi ga Manzon Allah (SAW) a wajen Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass da daya daga cikin mutanen ta shirya a Unguwar Kurna, kusa da Makwarari cikin birnin Kano .
Sai dai Alkalin Kotun Mai shari’a Atiku Muhammad Bello ya dage shari’ar zuwa yau Juma’a don ci gaba da sauraren shari’ar tare da bayar da umarnin tsare wadanda ake kara a gidan maza.
Abdul Inyass an ce ya yi wasu kalamai marasa kyau ga Ananbi Muhammad (SAW) a lokacin da wata mace mai suna Hajiya Zainab ta shirya Maulidin Shaikh Ibrahim Inyass a unguwar Kurna kusa da Makwarari cikin birnin Kano a ranar Alhamis din makon jiya.