Duk wanda ya rage teba za a ba shi kyautar zinari a Dubai
Yawan masu teba na karuwa a masarautar Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), don haka aka yanke hukuncin bayar da kyautar zinari ga duk wanda ya rage teba kyautar zinari, wanda kudinsa ya kai Dala 45 kan kowane kilo.Kamfanin dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, wadanda suka shiga wannan shirin tun a ranar 19 […]
Yawan masu teba na karuwa a masarautar Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), don haka aka yanke hukuncin bayar da kyautar zinari ga duk wanda ya rage teba kyautar zinari, wanda kudinsa ya kai Dala 45 kan kowane kilo.
Kamfanin dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, wadanda suka shiga wannan shirin tun a ranar 19 ga watan Yulin bana, an ba su wata guda su rauraye kibarsu. Cibiyar Pulitzer, ta bayyana yadda yawan masu teba ke karuwa a wannan birni, don haka ake ta bude gidajen sayar da abinci, a tsawon shekaru 20 da suka gaba. “Akwai matsaloli biyu da muka hango, fiye da rabin mutanen Dubai masu teba ne, kuma kimanin kashi 25 cikin 100 na mazaunan birnin sun bayyana cewa suna da matsala,” a cewar Philips na cibiyar binciken lafiya. Wadanda suka dace za su kimanin Dala dubu biyar, amma wannan ba wani kudi ba ne a wajen mutanen Dubai. Domin mafi karancin abin da suke samarwa na dukiyar kasa ya kai kimanin Dala dubu 45.