Duk wanda ya sa N5m a banki a sanar da EFCC —Majalisa

Za a soke rajistar duk cibiyar hada-hadar kudaden da ta ki sanar da EFCC kan ire-iren kudaden.

Duk wanda ya sa N5m a banki a sanar da EFCC —Majalisa

Majalisar Dattawa ta wajabta wa bankuna su rika sanar da Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) a rubuce game da duk mutumin da aka sanya kudin da ya kai Naira miliyan biyar a lokaci guda a asusun ajiyarsa na banki.

Majalisar ta kuma wajabta wa bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade su sanar da Sashen Yaki da Safarar Harmatattun Kudade na EFCC a rubuce game da duk wani kamfani ko hukuma da aka sanya kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 10 a asusunta a lokaci guda.

Sabuwar Dokar Sanya Ido Kan Safarar Haramtattun Kudade da Majalisar ta yi wa gyaran fuska ta wajabta “tarar N250,000 zuwa N1,000,000 ga cibiyoyin hada-hadar kudade da dangoginsu a duk lokacin da suka saba dokar.”

Dokar ta kuma haramta wa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade bude asusun ajiya mai dauke da boyayyen suna ko lambobi kadai ko sunayen bogi da dangoginsu.

Sashe na 12 na dokar ya tanadi tarar Naira miliyan 10 zuwa miliyan 50 kan duk lokacin da wata cibiyar hada-hadar kudade ta ki sanar da EFCC game kudaden da suka kai Naira miliyan 10 da aka sanya a asusun ajiyar wani kamfani ko wata hukuma.

Akwai kuma daurin shekara biyu zuwa biyar ga duk mutumin da aka ki sanar da EFCC idan aka sanya abin da ya kai Naira miliyan biyar a asusunsa na banki.

Za kuma a soke rajistar cibiyar hada-hadar kudaden tare da gurfanar da shugabannin gudanarwarta a gaban kotu.