Duk wanda ya sake kisan kai a Kaduna za a kashe shi – El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya gargadi jama’ar jihar cewa gwamnati ba za ta sake amincewa da kashe-kashen da ke faruwa a wasu yankunan jihar ba, inda ya ce duk wanda aka kama ya yi kisan kai shi ma ba za a kyale shi ba. Ya ce duk wata kungiya ko mutumin da ya […]

Duk wanda ya sake kisan kai a Kaduna za a kashe shi – El-Rufa’i
Duk wanda ya sake kisan kai a Kaduna za a kashe shi – El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya gargadi jama’ar jihar cewa gwamnati ba za ta sake amincewa da kashe-kashen da ke faruwa a wasu yankunan jihar ba, inda ya ce duk wanda aka kama ya yi kisan kai shi ma ba za a kyale shi ba. Ya ce duk wata kungiya ko mutumin da ya yi kisa gwamnati ba za ta kyale ba, shi ma zai dandani mutuwa.

Da yake jawabi ga wasu iyalai a gidan gwamnati, Gwamna El-Rufa’i ya ce tuni gwamnati ta ba sashin shari’ar na jihar iznin hukunta duk wanda ya aikata laifin.
Gwamnan wanda ke magana ta bakin kakakinsa Samuel Aruwan ya ce gwamnatinsa za yi kokarin ganin ta cika alkawuran da ta yi ga jama’ar jihar na sama masu da ribar dimokuradiyya.
“Wannan ne ya sa muke kira ga jama’ar Jihar Kaduna su guji kisan kai ko kai hare-hare a kan jama’a. Duk al’ummar jihar na da ’yancin zama cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba. Don haka wannan gwamnati ba za ta amince da kisan wani mutum a kan kowane dalili ba. Idan miji ya kashe matarsa shi ma zai fuskanci hukunci, idan mace ta kashe mijinta ko yaro ya kashe mahaifinsa ko mahaifiyarsa shi ma zai fuskanci wannan hukunci komai matsayinsa. Ba za mu taba amincewa da kisan jama’a ko mutum ba. Duk wanda ya aikata hakan shi ma ba za a kyale shi ba,” inji El-Rufa’i.
Gargadin na Gwamna El-Rufa’i ya zo ne kwana daya bayan da wani soja ya harbi wani direban tirela mai suna Abba Saminu a hanyar Kaduna zuwa Zariya saboda ya ki ba su cin hancin Naira 500.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa sojan ya harbi direban ne a kafa, kafin su yi tafiyarsu, kuma lamarin ya auku ne da misalin karfe 10:00 na dare a ranar Lahadi a kusa da wani gidan mai da ke kusa da Marabar Jos.
Majiyar ta ce a yayin da labarin harbin ya isa wurin direbobin tirela, sai suka tare hanya da manyan motocinsu domin nuna bacin ransu, kuma matakin nasu ya jefa matafiya a cikin matsala.
Direban da kwance a Asibitin Saint Gerald ya shaida wa Aminiya cewa: “Muna kan hanyarmu ta dawowa daga tafiya dauke da dankalin Turawa sai muka yi kicibis da sojoji a kan hanya da misalin karfe 10:00 na dare ranar Lahadi a daidai Marabar Jos. Sai suka bukaci in tsaya, bayan na tsaya ni da yarona sai suka ce mu ba su Naira dari biyar, ni kuma na ce ba ni da Naira dari biyar amma za a samu Naira dari. Jin haka sai suka yi mana tsawa cewa mu fito daga motar, bayan mun fito ne sai daya daga cikinsu ya mare ni da na ga haka sai na fita da gudu, sai kawai na ji karar bindiga nan take na fadi kasa. Ina kwance sai daya daga cikinsu ya zo yana salati da ya ga a kafa aka same ni, sai suka juya suka shiga motarsu suka bar wurin.”
Maigidansa wanda Aminiya ta tarar a asibitin, Alhaji Ibrahim ya koka a kan cin fuskar da sojoji ke yi wa direbobi a kan manyan hanyoyin kasar nan. Ya ce sojoji na damun direbobi da karbar cin hanci idan aka hana su kuma sai su wulakanta mutane. “Muna kira ga gwamnati da manyan sojoji su kawo karshen wannan matsala tsakaninmu da sojojin,” inji shi.
kokarin Aminiya na jin ta bakin Kakakin Sojojin a Jihar Kanar Abdul Yusuf ya ci tura domin bai amsa wayarta ba.
Sai dai Kakakin Gwamnan Jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i ya aike da Mataimakinsa da Kwamishinan ’Yan sanda wajen domin kwantar da hankalin dirobobi masu bore. Ya shawarci jama’a su guji daukar doka a hannunsu idan irin hakan ya auku.