Duk wanda ya yi fyaxe a Neja zai shekara 21 a gidan yari

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta amince da dokar daurin shekara 21 ga duk wanda aka samu da aikata fyade a a jihar a matsayin daya daga cikin matakan shawo kan wannan matsalar da ta zama ruwan dare.Shugaban Majalisar, Barista Adamu Usman ya ce, majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin gabatar wa […]

Duk wanda ya yi fyaxe a Neja zai shekara 21 a gidan yari

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta amince da dokar daurin shekara 21 ga duk wanda aka samu da aikata fyade a a jihar a matsayin daya daga cikin matakan shawo kan wannan matsalar da ta zama ruwan dare.
Shugaban Majalisar, Barista Adamu Usman ya ce, majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin gabatar wa Gwamnan Jihar Dokta Mu’azu Babagida Aliyu dokar domin ya rattaba mata hannu inda za ta zama madogara ga kotuna su rika yanke wannan hukunci ga duk wanda ya aikata wannan mummunan aiki.
Barista Adamu Usman ya nemi iyayen yara da aka yi wa fyade ko matan da aka yi wa fyaden su rika tanadar isassun hujjojin da za su taimaka wa masu bincike wato ’yan sanda da alkalai wurin zartar da wannan hukuncin ga mutanen da ya kwatanta da marasa imani.
Shugabar kungiyar Lauyoyi Mata reshen Jihar Neja, Malama Fati Takuma Sa’id ta yaba wa ’yan majalisar kan wannan mataki da suka dauka, ganin cewa aikata fyade ya zama ruwan dare da a lokuta da dama masu aikata wannan mummunan aiki kan yi takamar babu wani hukunci mai tsananin da za a iya zartar musu.
Malama Fati Sa’id ta ce, wannan wata dama ce suka samu na kara daura damarar sa kafar wando daya da wadanda suka mayar da fyade abin alfahari. “Don haka kungiyarmu za ta shiga sassan Jihar Neja domin wayar wa mutanen kai kan muhimmancin da ke akwai na gabatar da irin wannan matsalar ga ’ya’yan kungiyar domin bin kadin lamarin a hukunta masu hannu a aika-aikar.