Duk wanda ya yi ha’inci wajen ciyar da dalibai zai dandana kudarsa – Gwamna Bagudu

Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce duk dan kwangilar da ba ya ba da ingantancen abinci ga daliban makarantar da yake ciyarwa zai dandana kudarsa.Gwamna Abubakar Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da yake rangadin makarantun jihar domin gane wa idonsa irin abincin da ake bai wa dalibai a makarantun jihar.Gwamnan […]

Duk wanda ya yi ha’inci wajen ciyar da dalibai zai dandana kudarsa – Gwamna Bagudu
Duk wanda ya yi ha’inci wajen ciyar da dalibai zai dandana kudarsa – Gwamna Bagudu

Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce duk dan kwangilar da ba ya ba da ingantancen abinci ga daliban makarantar da yake ciyarwa zai dandana kudarsa.
Gwamna Abubakar Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da yake rangadin makarantun jihar domin gane wa idonsa irin abincin da ake bai wa dalibai a makarantun jihar.
Gwamnan Bagudu, ya kuma ce ban da ’yan kwangilar, gwamntinsa za ta sanya kafar wando guda da duk wani shugaban makaranta ko malami da aka samu yana rikon sakainar kashi da harkokin ilimi, musamman jin dadin daliban.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba, za a kira taron masu ruwa-da-tsaki a fannin ilimi, domin tattauna yiwuwar rge kudin kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) da dalibai ke bayarwa a farkon kowane zangon karatu, inda ya kara da cewa a makon nan gwamnatin jihar za ta fara rarraba littattafan rubutu da karatu kyauta a duk makarantun da ke jihar a yunkurinta na cika alkawarin da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.
Gwamna Bagudu ya fara zagayen gani da ido ne a makarantun da ke garuruwan Bunza da Kamba da Zagga da kuma dakingari.
A wani labarin kuma malaman makarantun firamare a Jihar Kebbi, sun bukaci gwamnatin jihar ta kawo karshen aikin tantance malaman da suka ce an dauki wata shida ana gudanarwa a makarantun firamaren da ke jihar.
Malaman wadanda suka bukaci a sakaya sunayensu, sun ce binciken ya sanya mafi yawansu a cikin matsala ganin cewa daga cikin bocar biyan albashi ce za a gyara, amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.