‘Duk wata Badeh na awon gaba da Naira miliyan 558 na sojin sama’

Wani shaida da Hukumar EFCC ta gabatar kan shari’ar da ake yi wa tsohon Hafsan Tsaro Iya Cif Mashal Alde Badeh, Iya Kwamanda Salisu Abdullahi mai ritaya ya shaida wa Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, cewa a lokacin da Badeh yake Babban Hafsan Sojojin Sama ya sha umartarsa da ya canja Naira miliyan […]

‘Duk wata Badeh na awon gaba da Naira miliyan 558 na sojin sama’

Wani shaida da Hukumar EFCC ta gabatar kan shari’ar da ake yi wa tsohon Hafsan Tsaro Iya Cif Mashal Alde Badeh, Iya Kwamanda Salisu Abdullahi mai ritaya ya shaida wa Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, cewa a lokacin da Badeh yake Babban Hafsan Sojojin Sama ya sha umartarsa da ya canja Naira miliyan 558 zuwa Dalar Amurka ya kawo masa gidansa.
Adadin wani bangare ne na kudin da suka saura na albashin wata-wata da ake biyan sojin sama, inji Kwamanda Abdullahi wanda shi ne Daraktan Kudi kuma Akantan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya daga watan Oktoban 2010 zuwa Disamban 2013.
Iya Kwamanda Abdullahi, wanda shi ne shaida na farko da Lauyan Hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya kira a shari’ar da ake yi wa Badeh, ya ce umarnin a canja kudin zuwa Dala ana ba shi ne da baki kamar yadda yake a al’adar sojoji.
“Muna karbar kusan Naira biliyan hudu domin biyan albashi. Jimillar kudin albashinmu a lokacin da nake Daraktan Kudi ya haura Naira biliyan biyu. Sauran kudin domin hakkokin ma’aikata ya kai Naira biliyan daya da miliyan 700. An kebe Naira miliyan 558 domin gudanar da harkokin mulki na ofishin Shugaban Ma’aikata duk wata. Yayin da sauran aka kebe su domin rarraba su ga sauran sassan sojin sama,” inji shi.
Ya kara da cewa:  “A lokuta da dama Babban Hafsan Sojin Saman yakan bayar da umarnin cewa a canja wannan adadin kudi zuwa Dalar Amurka a dauke su zuwa gidansa a sansanin hedkwatar rundunar sojin sama. Lokacin da aka canja wannan kudi aka kawo min nakan dauki wannan kudi ne zuwa gidan Babban Hafsan Sojin Sama da ke barikin Niger Barracks. Kuma a matsayinmu na jami’an soji ba mu neman a ba mu takardar shaidar cewa mun kai kudin. A wasu lokuta nakan shaida wa jami’in kudi ya same ni a gidan hafsan sojin sama na barikin Niger tare da kudin ta yadda zai gani da idonsa cewa na mika kudin ga Babban Hafsan Sojin Saman.”
Kwamanda Salisu ya ce: “Umarnin a canja kudin zuwa Dala ba a rubuce yake ba. Babban Hafsan Sojin Sama yana bayar da umarni da dama ba a rubuce ba. Umarnin da ake bayarwa a rubuce su ne wadanda ake bukatar a tura ofishinsa daga sauran rassa. Lokacin da aka nada ni Daraktan Kudi na iske Naira miliyan 120. Wani bangare ne na hakkokin ma’aikata da ake biya kowane wata. Amma na ki karba. Kuma na nemi a sanya kudin a karkashin kular Shugaban Ma’aikata domin kai ziyara da sauran al’amura.”
Tunda fako Babbar Kotun Tarayyar ta ki amincewa da bukatar Mashal Badeh na a dakatar da sauraron karar da Hukumar EFCC ta shigar a kansa. Lauyan Badeh, Mista Samuel Zibiri ya kalubalanci hurumin kotun da cewa akwai kura-kurai a tsarin.
Sai dai lauyan EFCC, Mista Rotimi Jacobs, ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar lauyan Badeh.
A hukuncin da ya yanke kan lamarin, Mai shari’a Abang ya ce babu tsarin da aka saba a shari’ar da ake yi wa tsohon Babban Hafsan Tsaron.
Ana zargin  Badeh ne da karkatar da kusan Naira biliyan hudu daga cikin kudin da aka ware wa rundunar sojin saman kasar nan a shekarar 2010 zuwa 2013.
Bayan ya shafe kwanaki a gidan kaso na Kuje, kotun ta bayar da belinsa a kan Naira biliyan biyu.