Dukan uwa ya haifar wa danta hadiye kusa a Jihar Edo
Wata mata ta lakada wa danta duka har sai da ya hadiye wata kusa da yake rike da ita a hannu yana wasa. Shi dai wannan yaro mai suna Mustafa Ali, wanda aka ce Uwar da ta haife shi ita ce ta fada shi da duka, har ya hadiye kusar a kan tana zargin ya […]
Wata mata ta lakada wa danta duka har sai da ya hadiye wata kusa da yake rike da ita a hannu yana wasa. Shi dai wannan yaro mai suna Mustafa Ali, wanda aka ce Uwar da ta haife shi ita ce ta fada shi da duka, har ya hadiye kusar a kan tana zargin ya dauke mata kudi N200, ya batar da su, wannan lamarin ya faru ne a makon jiya a garin Benin Jihar Edo.
Wadandalamarin ya faru a gabansu sun ce ita Zainabu Salihu Uwar, yaron ta fada wa wannan danta da duka, ta huce haushi tana mai cewa yaron ya sace mata kudi Naira 200, sai daga bisani aka ankarar da ita cewa yaron ya hadiye kusa da yake rike yana wasa da ita. A lokacin da take yi masa dukan sun ce sun gani ya jefa wani abu mai kama da karfe a bakinsa, kuma da alama ya hadiye shi, bayan an roketa ta bar dukansa ta ki, wahalar wannan dukan ta sa har ya hadiye kusar.
An ce da ta ji yaron ya hadiye kusa, daga nan kuma sai jikinta ya fara sanyi, ta koma tana tunanin ta kai shi asbiti, domin uban yaron ba ya gari, kuma kowa ya san illar da ke tattare da kusa a waje ma ballantana a cikin mutum, hakan ya tsoratar da ita maza ta dauke shi zuwa asibiti mai zaman kansa da ke unguwarsu.
Wakilin Aminiya ya yi tattaki zuwa wannan asbitin, kuma ya samu yaron kwance a gadon asibtin sai nishi yake, inda Dokta Douke, likitan wannan asibitin ya tabbata da kusar tana cikin yaron.
“Zai yi iya kokarinsa, tare da irin dabarunsu na likitoci ya ga kusar ba ta lahanta shi ba. Kuma zai bi hanya mafi sauki domin raba yaron da wannan kusar, har ya fitar da ita daga cikin sa,” inji shi
A nata bayanin Zainabu Uwar Mustafa ta ce “Wallahi ban yi masa duka ba, ban san da kusa a bakinsa ba.”