Dukan ‘yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta – Gwamna Dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe kuma mai neman tsaywa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Hassan dankwanbo ya ce dukan mutanen da suke neman takarar Shugaban kasa a karkashin PDP a 2019, sun fi Shugaban kasa Muhammadu Buhari cancantar shugabancin Najeriya. Gwamna dankwanbo ya bayyana haka ne a garin Jos, fadar Jihar Filato a […]

Dukan ‘yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta – Gwamna Dankwambo

Gwamnan Jihar Gombe kuma mai neman tsaywa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Hassan dankwanbo ya ce dukan mutanen da suke neman takarar Shugaban kasa a karkashin PDP a 2019, sun fi Shugaban kasa Muhammadu Buhari cancantar shugabancin Najeriya.

Gwamna dankwanbo ya bayyana haka ne a garin Jos, fadar Jihar Filato a ranar Litinin da ta gabata, a ci gaba da rangadin da yake yi na neman goyon bayan wakilan PDP a jihohin kasar nan.

Ya ce PDP ta horar da mutanen Najeriya da dama kan harkokin mulki da yadda za a warware matsalolin da suke damun ’yan Najeriya. Don haka kowane irin zabe za a yi a Najeriya, za ka ga ’yan PDP sun fito takara da yawa, domin sun cancanta sun kware kan tafiyar da mulkin  Najeriya.

Ya ce don haka aka samu ’yan takara da dama a jam’iyyar a shugabancin kasar nan. Kuma dukan wadannan ’yan takara na shugabancin kasa a karkashin PDP sun fi Shugaba Buhari cancantar shugabancin Najeriya.

Gwamna dankwambo ya kara da cewa ya cancanci ya shugabanci Najeriya, domin ya yi ayyuka a wurare da dama, kamar Babban Bankin Najeriya da Babban Akantan Jihar Gombe da na Najeriya, inda ya yi aiki, da Shugaba Obasanjo da ’Yar’aduwa da  Jonathan. Sannan ya yi Gwamnan Jihar Gombe a karkashin PDP, har karo biyu inda ya yi ayyuka da dama a jihar, musamman wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“A bangaren tsaro na yi kokari a Jihar Gombe, domin idan mutum ya tashi a mota daga Gombe zuwa Borno ba zai yi tafiyar minti 30 ba,  muna kusa da garin Maidugari muna kusa da dajin Sambisa. Mun yi makwabtaka da jihohin Taraba da Yobe amma duk da haka, mun yi iyakar kokarinmu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Jihar Gombe. Don haka ba mu samu matsalar garkuwa da mutane ba, ba mu samu matsalar fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma ba,”  inji shi.