‘Dukiyar Abacha’: Bayan muhawarar sai me?
Shin ko muhawarar da ta barke a kafofin sada zumunta bayan Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Najeriya Abubakar Malami ya ambaci wasu kudi da marigayi Sani Abacha ya “wawure” da “dukiyar Abacha” za ta zo karshe? Ministan dai ya sha suka daga ‘yan Najeriya da dama wadanda ke ganin kwatanta kudin da Abacha ya […]
Shin ko muhawarar da ta barke a kafofin sada zumunta bayan Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Najeriya Abubakar Malami ya ambaci wasu kudi da marigayi Sani Abacha ya “wawure” da “dukiyar Abacha” za ta zo karshe?
Ministan dai ya sha suka daga ‘yan Najeriya da dama wadanda ke ganin kwatanta kudin da Abacha ya waure, ko a ce “wawurar Abacha” da “dukiyar Abacha” tamkar wanke tsohon shugaban na mulkin soji daga laifi ne.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, cewa ya yi, “Ina farin cikin tabbatar da cewa ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020, Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta karbi $311,797,866.11 daga cikin dukiyar Abacha wadda aka dawo da ita daga Amurka…”
‘Abin da nake nufi’
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai ba shi shawara a kan al’amuran yada lamarai Umar Jibrin Gwandu, Malami ya ce ai tun da an riga an dawo wa Najeriya da kudin kuma sun shiga lalitar gwamnati, to sun zama dukiyarta, don haka ya ambace su da “dukiyar Abacha”.
Wata tambaya da wasu ‘yan Najeriya ke yi, wadda kuma ministan ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai ke nan, ita ce me za a yi da wannan kudi?
Shi dai Minista Abubakar Malami bai yi bayani ba a cikin sanarwarsa, amma mataimaki na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari a kan al’amuran yada labarai, Garba Shehu, ya ce an ma riga an kasafta yadda za a kashe kudin.
An gama kasafi
A wani sako da ya fitar, Malam Garba ya ce za a yi amfani da kudin ne wurin farfadowa da kammala wasu ayyukan raya kasa wadanda aka kwashe shekaru ba tare da an kammala su ba.
“Za a yi amfani da kudaden wurin farfado da tsoffin ayyukan raya kasa wadanda suka hada da Gada Kogin Neja ta Biyu, babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, babbar hanyar da ta taashi daga Abuja ta bi ta Kaduna ta wuce Kano; hakan zai samar da dimbin ayyukan yi da kuma inganta kwarewa da za su amfani kasar a ayyuka na gaba”.
An dai jima ana kasafta kudi don aikin Gadar Kogin Neja ta Biyu, amma kuma mai magana da yawun shugaban kasar bai fadi nawa aka narka zuwa yanzu da kuma nawa za a kashe nan gaba ba.
Ayyukan raya kasa
Sai dai ya kara da cewa za a yi amfani da wani bangare na kudin wurin kammala aikin samar da wutan lantarki a Mambilla wanda a cewarsa idan aka kammala zai samar da wuta ga gidaje miliyan uku kuma zai amfani sama da mutane miliyan 10.
Ya ce dawo da kudaden da ma wadanda aka karbo daga Ingila da Switzerland dama ce ta samar da cigaba a kasar da kuma cike guraben da sace kudaden suka haddasa a shekarun da suka wuce.
Ya kara da cewa dala miliyan 320 da aka dawo da su daga Switzerland a bara tuni aka fara amfani da su wurin ciyar da yara ‘yan makaranta, da tallafi ga miliyoyin ‘yan kasar da suka kowa talauci da kuma tallafin hatsi ga masu tsananin bukata.
Fahimtar juna
Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kasashe da dama sun ki amincewa su dawo da kudaden a karkashin gwamnatocin da suka shude ne saboda ba su gamsu da su ba, sannan ya jaddada cewa kudaden za su taimaka sosai a yaki da cutar coronavirus a kasar.
Ya ce an samu matukar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Amurka wanda hakan ya taimaka sosai wurin dawo da kudaden.
Garbe Shehu ya yi nuni da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta mai da hankali sosai a kan yaki da cin hanci da rashawa saboda tabbatar dawwamamiya cigaba a kasar.
Akwai ‘yan Najeriya dai da ke faragabar za a iya sake karkatar da wadannan kudade don haka suke ganin ya kamata a samar da wata hanya ta sanar da ‘yan kasa shiga da fitar su, komai yawansu kuma komai kankantarsu.