Dukiyar dangote ta kara habaka
Dukiyar mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka wato Alhaji Aliko dangote ta kara habaka zuwa Dala biliyan 15 da miliyan 400.An bayyana hakan ne cikin jerin mutanen da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta wallafa.dangote ya zama na 51 cikin jerin wadanda suka fi kudi a duniya idan aka kwatanta […]

Dukiyar mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka wato Alhaji Aliko dangote ta kara habaka zuwa Dala biliyan 15 da miliyan 400.
An bayyana hakan ne cikin jerin mutanen da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta wallafa.
dangote ya zama na 51 cikin jerin wadanda suka fi kudi a duniya idan aka kwatanta da bara inda ya zama na 67, a lokacin da mujallar ta kiyasta yawan dukiyarsa cewa ta kai Dala biliyan 14.7.
Shi ne mamallakin kamfanin siminti mafi girma a Afirka wato dangote Cement.
Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Afirka ma dan Najeriya ne Mike Adenuga, wanda ya mallaki Dala biliyan 10.
Nicky Oppenheimer, dan kasar Afirka ta Kudu shi ne na uku a jerin mutanen da suka fi kudi a Afirka, inda ya mallaki Dala biliyan 6 da miliyan 600.
Mujallar ta sanya Mista Adenuga na 103 a jerin wadanda suka fi kudi a duniya, shi kuma Mista Oppenheimer ya zama na 174.
Wasu daga cikin fitattun attajiran duniya na bana:
1. A bana ma Bill Gates mai kamfanin Microsoft ne ya zamo Attajirin Duniya da dukiyar da ta kai Dala biliyan 75.
2. Sai dan kasar Sipain da ke da kamfanin tufafi na Zara, Mista Amancio Ortega ya zo na biyu da Dala biliyan 67.
3. Fitaccen dan kasuwa Warren Buffet ya zo na uku da Dala biliyan 60.8.
4. Na shida kuma shi ne mai kamfanin Facebook, Mack Zuckerberg da ke da Dala biliyan 44.6.
5. A mata wadda ta fi kowacce kudi a duniya ita ce mai kamfanin sayar da kayan kwalliya
na L’Oreal Liliane Bettencourt wanda take da Dala biliyan 36.
6. Matashin da ya fi kowa zuba jari kuma shi ne, dan kasar Norway, Aledandra Andresen mai shekara 19 da yake da Dala biliyan 1. 2.
7. Tsohon da ya fi kowane tsoho zuba jari a duniya kuma shi ne, Dabid Rocketfeller mai shekara sama da 100 kuma ya mallaki Dala biliyan 3.