Dumamar yanayi (2)

Tun 1850 da aka fara daukar lissafin zafi, amma ba a yi zafi ba kamar na Janairu 2007, in an kwatanta da sauran shekarun da suka gabata, wannan ya tadawa masana yanayi hankali, a Caina da Indiya zaka ga wani hayaki da ke tashi da safe domin iska ya tsaya, wannan irin iskan ya fara […]

Dumamar yanayi (2)

Tun 1850 da aka fara daukar lissafin zafi, amma ba a yi zafi ba kamar na Janairu 2007, in an kwatanta da sauran shekarun da suka gabata, wannan ya tadawa masana yanayi hankali, a Caina da Indiya zaka ga wani hayaki da ke tashi da safe domin iska ya tsaya, wannan irin iskan ya fara zama ruwan dare a manyan birane duniya, wanda ya hada da Masar, Legas da Birazil. Ko a Kano akan ga irin wannan hayakin mai dauke da guda idan an dakatar da ababen hawa, musamman gab da Magariba.

Yanke bishiyoyi da ake yi, domin dumama daki, girka abinci, gyara gida da dai sauransu, ya sa iska ba ya kewayawa yadda ya kamata, sannan an sami narkewar kankara a yankin Antatika da Greenland, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa ake ganin cewa nan gaba za a dinga fuskantar ambaliyar ruwa a sassan duniya daban-daban, don ko a 2009 an kawo karan cewa kankaran na kara narkewa cikin sauri. Sannan a kasashe irin su Sudan akan sami wani hadarin zafi dauke kasa, wanda kan iya wa mutum kabari, yayin da ya taso sai a rika rufe shagunan da kofofin gidaje, ana buya!

Ta fuskar kulla da lafiya aka fara gabatar da dokokin hana sha taba a Turai wanda suka hada da kar a sha a asibiti, kasuwa, makarantu da sauran wuraren taron mutane kamar motar haya, musamman don kar a cutar da wanda baya sha, inda a wasu wuraren kamar filin jirgin sama, a kan kebe wani wuri, inda masu sha zasu hadu, su busa hayakin.

A dalilin sauyin yanayi ne aka fara samun yawa da raguwar wasu yanayin da aka saba da su, kamar karancin ruwan sama a wasu wurare, da yawan ruwan a wasu sassan duniya, wanda haka kan yi sanadiyar ruwa zai cinye garuruwan da suke a gabobi, mu dubi Tsunami na karshen 2004 a yankin Asiya, wannan na daya daga cikin abubuwan al’ajabi a kwanan nan, ruwan tsufana, wanda a kwanki kadan sai da ya yi sanadiyar rasuwar mutane sama da dubu dari uku. Katarina da ta faru a Amurka a 2005 da wani iska da ya isa Gabas ta Tsakiya a kwanan nan, sannan ana samun janyewar ruwa a wasu sassan duniyar, kamar a Ghana, inda madatsar ruwan da take ba kasar wuta, na rage karfi a bisa dalilin cewa ruwan ya yi kasa.

Wajen warware matsalar dumamar yanayi ne aka fara kera motoci masu shan mai kadan, ko rage aiki da man fetur mai wari da hayaki, inda aka kirkiro sarrafa mota ta hanyar amfani da kayan abinci kamar man gyada, ko ruwan rake, da dai sauran sinadaran da kan iya daukar nauyin tafiyar da injuna.

Bayan an yi wani taron duniya don kara wa juna sani game da yadda dumamurwar yanayi take yin barazana, aka tashi da cewa, ko ba a yi komai ba wata rana duwatsun nan tauraro mai wutsiya na iya kawo babbar barna ga duniya, domin a kwana a tashi dole wani ya fado kan duniya.

A kwanan nan in muka lura za mu ga cewa damina ta sauya, a yi ruwa a lokacin da ya saba al’ada, watannin ruwan kuma sai a yi kwanaki ba a yi ruwa ba, sannan hadari ya zo ya wuce, zafi ya karu, duk da cewa ana camfi cewa zunubi da fasadi sun yi yawa, amma a zahiri wadannan ba su isa su zama dalilai ba, domin akwai kasashen da ake aikata alfasha a fili, amma kullum sai an yi musu ruwan sama! A ilimin yanayi sauyin shekara da bambancin saukar damina ma’aunai ne na gwajin jinkiri da gaggawar saukar ruwa, yayin da wasu ababe da suka zama dabi’a suke sauyawa a wasu dalilai kamar shishigen bil-adama da ‘yan neman kokof.

Taron shugabannin duniya kan kawo saukin dumamar yanayi ya tashi ba tare da kasa daya ta amince ta rage yawan babura da injuna don rage hayakin dake gurbata sarari, domin ba kowace kasa ke amfani da jiragen kasa ba ko na karkashin kasa balle a sami saukin. Inda aka yi baram-baram kowa ya koma kasarsa. Babban barazanar dumamar yanayi ga bil-adama shi ne rage albarkar abinci, babu tsaro, tsaron cimaka, ba koshi ko an yi noma, sai an yi yunwa don yawan mutane da tsananin bukatar kayan gona ga rayuwar dan Adam.

Yanayin ya kara tabbatar mana da cewa duniyar ta kusa tashi, musamman wajen samu da aiki da makamin nukiliya, wanda wasu na aiki da shi wajen saraffa wutar lantarki, kulla da lafiya, sannan wasu manema yaki na iya tada makami mai guba a wata kasa, ko ya kai ga ‘yan ta’adda, ko juyin mulki a wata kasa wani ya harba nasa, a  duniyar da masu makamin na karuwa, tabbas wata rana wani zai gwada nasa!

Buhari Daure [email protected] Modoji, Katsina.