Dumu-dumu Muzu-muzu

Shugabannin Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge, sun jirga kansu, musamman ganin yadda Dumu-dumu Muzu-muzu ya dare bisa karagar jangabanta, bayan an bangaje Banga-banga Tukururu, kuma ga shi an aiwatar da tsarin kama-karya, tauna cinye ka hadidiye a zabi-sonka na fitar da ’yan takarar da za su fafata da ‘ya’yan giwar jam’iyyar adawa. Mai […]

Dumu-dumu Muzu-muzu

Shugabannin Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge, sun jirga kansu, musamman ganin yadda Dumu-dumu Muzu-muzu ya dare bisa karagar jangabanta, bayan an bangaje Banga-banga Tukururu, kuma ga shi an aiwatar da tsarin kama-karya, tauna cinye ka hadidiye a zabi-sonka na fitar da ’yan takarar da za su fafata da ‘ya’yan giwar jam’iyyar adawa. Mai dan boto ta tsayar da Mai Jona-tantin mulki, don a ci gaba da Gudun-loko, inda giwar adawa ta tsayar da ja-gaban masu fafutikar Burin-huriyya a matsayin dan takarar shugabancin al’ummar Haurobiya.
Mai dan boto da sanda jirge a karkashin jagorancin Dumu-dumu Muzu-muzu ta tafka ta’asa a kwanon tasarta, domin ’ya’yanta ma Kukan Tenhiyarsu ya karu, tun da Haurobiyawa sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda ake jan ragamar kasa, inda ta karke da jan rigima. Domin a tsakanin shekara ta dubu sili da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa zuwa shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya da mai dan boto ta shafe tana jan akalar kasar nan, Haurobiyawa sun dandani kudarsu, inda aka dade ana kada musu jauje a gangar jiki da karatun wasikar auran gida da na daji. Baba-ojo ya zo ya yi rawar banjo a kan Haurobiyawa; shugaba ’Yar’bishiya ya kama ragama a halin laulayi, inda ya kai gargara a kan laulawar rashin koshin uwar jiki. Don haka da aka fara gudu a cikin loko da al’umma sai kowa ya rasa inda aka dosa.
Haurobiyawa na da masaniyar cewa, Tumun-fullo da Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku, wadanda jiga-jigan ’yan Hauren-Danja ne sun yi ikirarin tada kayar baya matukar Haurobiyawa suka ki yarda a ci gaba da Gudun-loko da Jona-tantin mulki da su.
Batu na ingarman karfen karafa, in har daukacin al’ummar Haurobiya za su yi la’akari da gazawar da mai dan boto da sanda jirge ta nuna a tsawon shekaru sili da babban lauje da ta yi, tana ta ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege wajen ririta dukiyar Haurobiya, inda shugaban kasa ya yi nuni da cewa, samartakar kusu da halin jaba da watandar Hauro da ake tafkawa, wai “ba kwashi kwaraf ba ne, tun da duk abin bai wuce gafiya ta tsira da na bakinta ba.” Kuma a tsawon wadannan shekaru Haurobiyawa sun zauna a cikin Jamhuriya ja-ni-ina-reto, wadanda ba su samu wuri rakabawa ba, sun samu kansu a cikin ‘Duhun-dundum-durundum, inda ake ta yi musu cin duhu.’
Jiga-jigan mai dan boto da sanda jirge, sun karya lagon Hukumar yaki da watandar lalita da ake yi a kasar nan. Rubdugau ya zo, ya yi gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dabara; ita kuwa uwargida Mai Fari da na-mujiya, da ta yunkuro sai kawai aka kawar da ita; Shi kuwa Loma-a-murde tuni ya zama ‘Muzurun-Lami.’
Masanin Sisi-da-sisi a lokacin yana rike da ragamar Babban Asusun Haurobiya, sai ya bankado badakalar yadda aka yi sabi zarce da damin Dalar Hauron Amurkawa har gashin balama karamin lauje da zagaye, wadanda aka yi zagayen dan wake da su. Saboda haka aka yi masa bakam, yana zuwa kasar Niyyar-jari, wani taron kara wa juna sani, sai suka wafce mukaminsa. Shi kuwa Mai-duka ya yi masa sakayya da mukamin Babban mutum mai rawani na birnin Dabo.
Sannan idan mutum ya ce yana son jera sunayen wadanda suka yi wadaka da dukiyar al’umma, to tabbas zai gaji da tatara sunayen su Santalla kwaiduwa, wadda ta arce da damen Hauro kula da filin saukar tsuntsayen sama; ga Baudadden Joji da Aminin Dabo, wadanda suka yi watanda a tashar kwale-kwalen Haurobiya; ga Uwargida Mai dama Fate-fate, wadda ta yi sabi arce da damin Hauro a Majlisar Rafkiyar wakilan Haurobiyawa; ga Mace da zane, wadda ke damawa a cikin tunkuzar man Haurobiya; ga kwantiragin bogi da aka bai wa Tumun-fullo da Asara-dan-kwabo, wai don su dakile bumburutu buruntun satar mai, alhalin su ne gwanayen wannan aika-aika, kuma ana zargin ma baya ga afuwar da shugaba ’Yar’bisiya ya yi musu, ai tubar muzuru kawai suka yi.
Tsarin dama-dama-da-kurda-kurdar wasan-Samson –siya-siya a siyasar Haurobiya kusan a iya karkarewa da cewa, ya jefa al’umma cikin tsomomuwa. Domin wasu ’yan tsiraru ne kawai ke damawa, inda gama-garin al’umma ke fama da wahalhalun rayuwa, wadanda suka hada da rashin koshin uwar jiki, saboda tsallen badaken Bokayen Turai da Allan bakun da direbobin alli ke yi da hukuma wajen neman karin ladar kwadago. Kai tsilli-tsillin matsalolin da Haurobiyawa ke fama da su sun haura tarin shurin masaki!
Ga shi tsawon shekaru kasar nan na fama da yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko. Wannan yamutsin ya sanya Baraden Burgar Gadi har rance suka rika yi a lalitar kolo. Su kuwa masu dan kulki da tambarin giwa like a tagiya, babu abin da suka kware a aki sai karbar ’yan kwabbai a kan hanyoyi masu kwazazzabai, inda masu jan linzamin ababen hawa ke dan difara musu Hauro babban lauje da zagaye, kodayake a da dai suna karbar karamin lauje da zagaye, amma dai an kara farashi. Wanda duk ke inkarin wannan batu, to sai ya tuntubi ’ya’yan kungiyar Natuwo, masu laluben na-koko a jikin kurkurido da shorido.
Lokaci ya yi da Haurobiyawa za su fasko cewa, Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge ta kassara kasar nan, kodayake dai an yi kaikayi koma kan mashekiya. Domin su ma suna cikin rikici, inda masu murdiyya da danniyar da zabi-sonka suka mayar da ’yan takararsu, suka zama ’yan taka-kara.
A matsayina na babban direban allin wannan farfajiya, ina ganin lokaci ya yi da Haurobiyawa, masu hankali a kwanyarsu, ba masu hankali a hannun taguwa ba, za su yanke hukuncin zaben Jam’iyyar mai maganin ciwon kai, ta yadda za a gabatar wa shugaban fafutikar Burin-huriyya dimbin al’amuran da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya, shi kuma ya yunkura wajen warware kowace irin badakala. Saboda haka kowa ya riki tsintsiya mai kwakwa don share dimbin kazantar da mai dna boto da sanda jirge ta tara wa al’umma. Idan an kammala shara, sai kuma a zo a sake bi da tsintsiya ’yar laushi. Yin haka ya zama wajibi, domin ko a sana’ar na-duke kowa ya san cewa ana yin ‘mai-mai.’ Ita dai gayauna, an ce sai da gewaya. Saboda haka kowa ya dauri aniyar shuka alheri, mu kuma yi ta gewayen alheri, don ta haka ne za mu mori irin alheri, mu mayar da mugun nufin mai dan boto ya zama cikin kwandon sharar labaran da, da na yanzu!
Su Dumu-dumu Muzu-muzu, sai su je can a yi ta yi musu muzu-muzu ko lage-lage, har a samu a daure su tamau da lage. Kuma yadda aka bangaje Banga-banga tukururu, haka muke fatan a lalalga Dumu-dumu Muzu-muzu, a wajen yi masa lage-lage ko muzu-muzu; ita kuwa mai dan boto da sanda jirge, muna fatan ta zama gunzu, idan za a rabata gida karamin lauje, shagabanninta kuma a yi ta kada musu juje!