Dunga ya yi alwashin dawo da martabar Brazil
Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Brazil Carlos Caetano Bledorn berri, wanda aka fi sani da Dunga ya yi alwashin dawo da martabar Brazil.Dunga shi ne Kyaftin din Brazil yayin Gasar Kofin Duniya ta shekarar 1994, kuma shi ne Kocin Brazil daga shekarar 2006 zuwa 2010.“Na yi matukar farin cikin sake dawowa. Na yi alwashin […]

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Brazil Carlos Caetano Bledorn berri, wanda aka fi sani da Dunga ya yi alwashin dawo da martabar Brazil.
Dunga shi ne Kyaftin din Brazil yayin Gasar Kofin Duniya ta shekarar 1994, kuma shi ne Kocin Brazil daga shekarar 2006 zuwa 2010.
“Na yi matukar farin cikin sake dawowa. Na yi alwashin dawo da martabar Brazil a fagen kwallon kafa.” Inji Dunga mai kimanin shekara 50.
Dunga ne ya maye gurbin Luiz Felipe Scolari, wanda ya yi murrabus bayan Brazil ta kasa kai wa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2014, bayan kasar Jamus ta lallasa Brazil da ci 7-1.