Duniya Mai JuyiDuniya Mai Juyi
Idan dai dan Adam na da rai babu abin da ba zai gani ba. Shi ya sa Bahaushe ke cewa,’ kowa ya dade zai ga dadau,’ domin kuwa abin da yake ta ba shi tsoro watan wataran zai komo yana ba shi mamaki. Yanzu wa zai yarda da cewa Cif Edwin Kilak, babban shugaban ‘yan […]
Idan dai dan Adam na da rai babu abin da ba zai gani ba. Shi ya sa Bahaushe ke cewa,’ kowa ya dade zai ga dadau,’ domin kuwa abin da yake ta ba shi tsoro watan wataran zai komo yana ba shi mamaki. Yanzu wa zai yarda da cewa Cif Edwin Kilak, babban shugaban ‘yan siyasar yankin Neja-Delta ya fice daga cikin jam’iyyar PDP, ya kuma wanke wa tsohon shugaba Jonathan hannu aka? Wanda duk ya ji wannan labarin zai zaci cewa bai ji da kyau ba, ko kuma ya dauka kunnensa ne ke zagi. Dalili kuwa shi ne ko rantsuwa aka ba mutum zai saba laya cewa da Edwin Kilak da jam’iyyar PDP ai takalmin kaza ne, mutu ka raba. Shi ne ruhin jam’iyyar, kuma wanda ya zame ja-gaban ‘yan yankin Neja-Delta wajen tozarta al’umman Arewacin kasar nan, wadanda shi da jama’arsa ke kira almajirai kuma kidahumai, marasa kunan ci gaban kasar nan, masu taka mata birki yayin da take yunkurawa don kai wa ga kasaita.
A lokacin yakin neman zaben da ya wuce Edwin Kilak ne ya kasance ubangidan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, domin kuwa goya shi ne a bayansa kawai bai yi ba, amma duk wata tarairaya da nuna goyon baya ya gwada masa, ya kuma daure masa gindi, har yana toroko da kumfar baki cewa idan har mutanen Arewa suka dakile yunkurin Jonathan na komawa bisa kujerarsa, to sama da kasa za su hade, kuma matsalar da hakan zai haddasa akan ‘yan Arewa za ta kare. Haka nan Cif Edwin Kilak, wanda ‘yan Arewa ke yi wa lakabi da tsohon Najadu ya yi ta yi wa ‘yan tsagerun yankin Neja Delta jagora, irin su Mujahid Asari Dokubo, suna yi wa Muhammadu Buhari jafa’i da tujara, kuma ba irin cin kashin da ba su yi masa ba don dai kawai yana takara tare da dan lelensu, Goodluck Jonathan.
Kwatsam, rannan sai ga labari cewa Cif Edwin Kilak ya yi hannun riga da jam’iyyar PDP, kuma ga shi can yana tozarta tsohon Shugaba Janatan a matsayin talasurun da ya kasa hana rashawa da cin hanci a zamaninsa, saboda bai iya tsawata wa wasu kangararrun jami’an gwamnatinsa masu yi masa mazuran da ke razanarwa har hantarsa na kadawa. A cewar Edwin Kilak, Jonathan na ji, yana gani, ya kasa maganinsu, suka kuma yi ta wadaka da dukiyar talakawa ba abin da ya iya yi. A cewarsa kuma irin mulkin tsohon Shugaba Janatan shi ake kira kantafi, masomin asara, domin kuwa ya jefa Najeriya cikin badakalar da ta tsiyata ta, jami’anta kuma suka tagayyara ainun.
To, wai duk da wannan tereren da Edwin Kilak ya yi wa dan morinsa, sai ga shi nan daya daga cikin mutanen da ya tozarta yana ta kwanzarta shi, kai ka yi tsammani ba sauran wani mutumin kirki a duniya face tsohon shugaba Janatan. Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan Ilmi a zamanin Janatan din, watau Alhaji Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ya fito fili, firi-falo, yana cewa babu wani da a fadin sararin duniyar nan da ya kai Janatan daraja a idanunsa, sa’anan kuma shi bai yi nadamar aiki a karkashinsa ba, kuma har ya koma ga Mahaliccinsa ba zai daina daukaka matsayin Janatan ba, domin kuwa babu wanda ya fi shi shimfida wa Najeriya abubuwan alheri, babu kuma wanda ya fi shi dacewa da jan ragamar mulkinta kamarsa.
Tirkashi, wai an ce da Makasau bawa! Wai shin wane hawa, wane gangare ne Shekarau ya gano da zai dauki mutumin da ubangidansa, ko kuma a ce ubangoyonsa ya watsar, shi kuma ya karkade masa kura, sa’annan ya goya shi? To, ai an ce wanda ya goya kare shi ya san yadda zai yi da bakinsa. Anya kuwa Shekarau zai iya jure halayen da suka sanya ‘yan Najeriya suka juya wa gwarzonsa baya, sa’annan kuma jama’arsa suka dawo daga rakiyarsa tun asuba na Maiduguri? Ai ba abin mamaki ba ne idan har Edwin Kilak ya yaba da kwazon Shugaba Muhammadu Buhari na yaki da rashawa da cin hanci a kasar nan, abin mamakin kawai shi ne yadda Shekarau ya gamu da batar basira, domin kuwa ga shi nan ana raba shi da kiwon akuya, yana kyalla ta haihu. Da wane dalili ne zai rungumi mutumin da aka gama yayinsa, wanda kuma kowa da kowa ke zarginsa dangane da sakaci ko sakarcinsa na barin al’amuran Najeriya su balbalce? To, ai ba mamaki game da haka, domin kuwa gwanayen magana na cewa komai lalacewar tsumma akwai wanda ke so, zai kuma dauka. Tsohon shugaba Janatan dai kara-da-kiyashi ne, kuma tsohon gwamna Shekarau ya dauka da saninsa.
Sanin kowa ne tsohon gwamna Shekarau ya dade yana kawazuccin zama shugaban kasa, ko ta halin kaka, kuma babu irin abin da bai yi ba don bakanta Muhammadu Buhari kada ya zama shugaban kasa, amma duk a banza, ta Allah ba tasa ba. Shi ya sa ya dinga yi wa Buhari zagon kasa da kulle-kulle don kar ya samu sukunin yin takara a jam’iyyar ANPP a 2011, saboda shi ke son a tsayar da shi. Tsananin kuntatawar da shi da abokan makircinsa, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Yariman Bakura da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, dalhatu Bafarawa suka yi wa Buhari ta sa shi ficewa daga cikin jam’iyyar ANPP, ya kafa wata sabuwa fil, watau CPC, ya bar wa su Shekarau kayan tsiyarsu. Amma me ya faru daga bisani? An tsayar da Shekarau takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ANPP a 2011, ya kuma fafata da Buhari da ke jam’iyyar CPC. Ai nan take Shekarau ya fahimci cewa ruwa fa ba sa’an kwando ba ne, domin kuri’un da ya samu, dubu dari takwas ne kacal, a dukkan sassan kasar nan, kuma da kyar suka haura ‘yar doriyar da Buhari ya samu na miliyan goma sha biyu da dubu dari shida.
Amma duk da haka nan Shekarau ya kasa gane cewa abin da ya shuka ne ya girba, kuma ga shi nan a wannan karon bayan ramukan muguntan da shi da makararrabansa suka hahhaka wa Buhari a zaben da ya gabata bai afka ciki ba, sai kuma suka ki rurrufewa, to kada kowa ya ji mamaki idan Shekarau fada ciki, bayan jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takararta a shekarar 2019, kamar yadda ta ce tana son tsayar da wani baragurbin dan Arewa a zabe mai zuwa. O, duniya mai juyi, wai kwado ya fada ruwan zafi? Me kuma Shekarau zai ce idan ya fada ramin da ya haka da kansa? Oho!!!